Labarai

Hasalallun Sanatocin APCn da su ka faɗi zaɓen fidda-gwani sun gana da Buhari

Wani gungun hasalallun Sanatocin APC su 22 da sakamakon yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani bai yi masu daɗi ba, sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanatocin waɗanda Balalliyar Majalisar Dattawa Uzor Kalu ya yi masu jagora, sun ziyarci Buhari inda su ka nuna masu damuwar su tare da kurarin barazanar ficewa daga APC.

Musamman sun bayyana masa yadda aka riƙa yi masu rashin adalci da kuma yadda gwamnoni su ka wawure zaɓen fidda gwani ya koma zaɓen ‘yan gaban goshin gwamna.

Tuni dai Sanatoci da dama sun fice daga APC su ka riƙa tururuwa zuwa PDP da NNPP.

Sannan kuma farkon makon jiya ne Shugaban Jam’iyyar ANPP Abdullahi Adamu ya je Majalisar Dattawa ya nuna damuwar sa ganin yadda sanatoci da manyan ‘yan takara ke ficewa daga APC, bayan zargin yadda gwamnonin jihohi su ka yi hajijiyar rashin adalci da su a lokacin zaɓukan fidda-gwanin APC.

Tuni dai Sanata Babba Kaita wanda shi ne Sanata mai wakiltar yankin Shugaba Muhammadu Buhari, wato yankin Daura, ya fice daga APC ya koma PDP, kuma ya tsaya mata takarar sanata a can.

Shi ma Adamu Aliero ya fice ya koma PDP kuma yanzu haka a ƙarƙashin PDP ɗin zai sake yin takarar sanata ɗin.

A yayin ganawar kafin Buhari ya kimtsa ya tashi zuwa ƙasar Portugal, ya shaida masu cewa su yi haƙuri gaskiya za ta yi halin ta.

Ya kuma sha masu alwashin cewa zai shiga lamarin domin ganin an daidaita al’amurra. Kuma yaba su haƙurin cewa a ajiye batun canja sheƙa.

Bayan fitowar su, Sanata Kalu ya shaida wa manema labarai cewa a yanzu hasalallun sun huce, sun haƙura da canja sheƙa.

Sai dai kuma ba a san irin sakayyar da za a yi masu ba, tunda ba za su wakilci APC a zaɓen 2023 ba.

Premium Times ta buga labarin zuwan Shugaban APC domin ganawa da Sanatocin APC kan magance fitar-farin-ɗango da ake yi daga jam’iyyar.

Ganin yadda hasalallu daga sama har ƙasa ke ci gaba da yin fitar-farin-ɗango daga APC zuwa wasu jam’iyyu, Shugaban jam’iyya mai mulki Abdullahi Adamu ya garzaya Majalisar Dattawa domin yin ganawar sirri da Sanatocin APC, a ƙoƙarin shawo kan ci gaba da ficewar da ake yi a kullum.

Adamu ya isa Majalisa kusan ƙarfe 2 na yammacin Laraba, inda ya yi ganawar sirri da Sanatocin.

Bayan ya fito, ya shaida wa manema labarai cewa canjin sheƙar fitar-farin-ɗango da ake yi daga APC abin damuwa ne.

Ya ƙara da cewa dalili kenan ya je Majalisar Dattawa ya gana da Dattawan APC, domin shawo kan lamarin.

“Shugabannin jam’iyya na ƙoƙarin samo hanyar hana ci gaban ficewar. Babu jam’iyyar da ba a fita. Amma an fi zuzuta ficewar da ake yi daga APC. Amma duk da haka mun damu sosai, saboda ruwan da ya doke ka, shi ne ruwa.”

An fara rubdugun ficewa daga APC tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, inda aka riƙa ƙorafin yin rashin adalci da maguɗi tun daga sama har ƙasa.

Shi kan sa Adamu ana zargin sa haddasa rikicin da ke faruwa yanzu, wanda APC ta miƙa wa INEC sunan Sanata Ahmad Lawan wanda bai tsaya takara ba, maimakon sunan Basheer Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na mazaɓar Lawan.

Kusan sati ɗaya kenan a kullum sai Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana ficewar aƙalla Sanata ɗaya daga APC.

Cikin hasalallun Sanatocin da su ka fice daga APC sun haɗa da Shugaban Masu Rinjaye, Yahaya Abdullahi, Adamu Aleiro, Francis Alimekhena, Babba Kaita mai wakiltar Mazaɓar Shugaba Buhari, Halliru Jika da kuma Lawan Gumau.

Wannan jarida ta kuma buga yadda zaɓen fidda-gwani ya janyo ficewar jiga-jigan APC a Katsina, Sokoto da Bauchi.

A Jihar Bauchi manyan APC su shida, waɗanda su ka haɗa ‘yan Majalisa da tsohon mataimakin gwamna, sun fice daga jam’iyyar APC a jihar Bauchi. Kuma ba su kaɗai su ka fice ba, har da ɗimbin magoya bayan su duk su ka yi gaba, su ka bar APC cikin ruɗani a Bauchi.

Ficewar manyan APC daga jam’iyyar a Bauchi ya kawo cikas ƙwarai ga ƙoƙarin da ta ke yi na karɓe mulki daga hannun PDP, wadda Gwamna Bala Mohammed ya sake tsaya mata takara, domin ya kammala zangon sa na biyu kuma na ƙarshe.

Guguwar canjin sheƙa ko guguwar ficewa daga APC ba a Bauchi kawai ta tsaya ba. Hasalallu daga jihohi daban-daban na ci gaba da yin tururuwar ficewa daga APC su na shiga wasu ‘jam’iyyun daban.

Babban dalilin ficewar mafiya yawan su shi ne zargin rashin adalcin da su ke cewa an tafka masu yayin zaɓen fidda-gwani.

Hasalallun Da Suka Fita APC A Jihar Bauchi:

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Lawal Gumau ya fita daga APC ya koma NNPP, bayan ya kasa lashe zaɓen fidda-gwani.

Shi ma Sanata Halliru Dauda ya canja sheƙa, bayan ya kasa cin zaɓen fidda-gwanin takarar gwamna.

Sai kuma Ɗan Majalisar Tarayya na Bauchi, shi ma ya fice bayan ya kasa cin zaɓen fidda gwani.

Tsohon Mataimakin Gwamna, Abdu Sule ya fice saboda abin da ya kira rashin dattako da rashin sanin ya-kamata da ake nunawa a APC.

Akwai Farouq Mustapha, Ibrahim Mohammed da sauran su.

Katsina: Yadda NNPP Ta Kwashi Lodin Mutanen Buhari:

Akwai Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Malumfashi/Ƙafur, Babangida Talau, Armaya’u Kado mai wakiltar Dutsin-Ma/Kurfi, Aminu Ashiru mai wakiltar Mani/Bindawa.

Hadimin Aminu Abdulƙadir mai suna Bature Ibrahim ya ce “Oga na zai sake shiga takara ya kare kujerar sa a ƙarƙashin NNPP.

Shi kuma Talau takarar Sanata ya fito a ƙarƙashin NNPP a shiyyar Sanatan Katsina ta Kudu.

Akwai tsoffin ‘yan takarar gwamna biyu, Umar Abdullahi (Tata) da Garba Ɗanƙani, duk sun fice daga APC.

Umar ya koma PDP, shi kuma Ɗanƙani takarar gwamna zai yi a ƙarƙashin AA.

A Sokoto Guguwa Ta Yi Wa APC Ɓarna:

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gwadabawa/Illela, Abdullahi Salame ya sha kwaramniyar rikicin neman neman ƙwato APC daga riƙon laya hannun ɗan damben da Sanata Aliyu Wamakko ya yi mata. A yanzu dai Abdullahi ya koma PDP.

Ɗan Majalisar Tarayya Isa Kurdula ya koma PDP, shi ma Bello Jibrin tsohon Ministan Al’adu da Yawon Buɗe Ido ya koma PDP.

A Katsina, kwanan baya PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa ɗan’uwan Buhari ya yi rantsuwar tarwatsa APC.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Sandamu/Daura/Mai’aduwa, Fatuhu Muhammad, ya yi barazanar tarwatsa jam’iyyar su APC, a Jihar Katsina.

Fatuhu wanda Shugaba Muhammadu Buhari kawun sa ne, kuma sun yi kama da juna sosai, ya yi barazanar komawa jam’iyyar NNPP, sakamakon abin da ya kira rashin adalcin da ya ce an yi masa wajen kifar da shi a zaɓen fidda gwani.

Wani mai suna Aminu Jamo ne ya kayar da Fatuhu da ƙuri’u 117, shi kuma Fatuhu ya samu ƙuri’u 30 kacal.

A cikin wata magana da Fatuhu ya yi ta waya, shi da wani kuma aka riƙa watsa rikodin ɗin maganar, Ɗan Majalisar ya yi iƙirarin cewa fashi aka yi masa, kuma sai ya ƙwato haƙƙin sa, ko kuma ya fice daga jam’iyyar.

Hirar wadda ke da tsawon minti 6 da sakan 22, PREMIUM TIMES ta saurari inda Fatuhu ke magana da wani da ya ke kira Ranka Ya Daɗe, ya na ce masa sai ya tarwatsa APC a Jihar Katsina.

Ya ce shi ba zai tsaya sake wani zaɓen fidda gwani ba, ko ma da jam’iyya ta ce a sake ɗin. Saboda shi ne wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin da aka yi, amma aka danne masa.

“Ba za su iya sake wani zaɓe ba. Saboda ni na yi nasara a zaɓen farko da aka yi. Sun karya doka. Don haka a ba ni takara ta. Ko mu haɗu a kotu, ko kuma na tarwatsa APC, na kawo wata jam’iyya a Daura.” Inji shi.

“Zan fa iya rungumo jam’iyyar nan ta Kwankwaso mai kayan marmari na kai ta a Daura.

“Zan iya kai NNPP a Daura, saboda kowa kan sa kawai ya ke so. Su zo su bayyana abun da su ka yi wa talakawa, ni ma na kawo abin da na yi masu, a ga wanda mutane za su bi.” Inji Fatuhu.

Fatuhu ya ce idan ya tashi tsiyar sa, ba a Daura kaɗai garin Shugaba Buhari zai tarwatsa APC ba, har da cikin jihar baki ɗaya.

“Na rantse sai na tarwatsa APC a Jihar Katsina, saboda ɗan takarar NNPP na zaɓen gwamnan Jihar Katsina, Nura Khalil da mutanen sa na jira na.

“Ba zan bari wasu su ƙuntata min ba. Saboda idan da mulkin nan gado ne, ai da ni ne zan gaji Shugaba Buhari, Saboda ni ne ɗan uwan sa na jini.”


Source link

Related Articles

8 Comments

 1. Hmm it appears like your blog ate my first comment (it was super long)
  so I guess I’ll just sum it up what I submitted and say, I’m
  thoroughly enjoying your blog. I as well am an aspiring
  blog writer but I’m still new to the whole thing. Do you
  have any tips and hints for newbie blog writers? I’d
  really appreciate it.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button