Nishadi

HATTARA: Kada a fada tarkon masu zambar wai ana buga cacar samun bizar zama a kasar Canada

Wani sako da ke yawo a sakonnin ‘WhatsApp’ dake kira ga ‘yan Najeriya da ke neman samun bizar shiga kasar Canada na shekarar 2021/2022 ta hanyar cacar da ake yi a yanar gizo wato Canadian Visa Lottery Online a turance su cika fom domin samun wannan dama. A cewar sakon, wannan ce hanya da ya fi sauri da sauki na samun bizar ga duk wadanda ke sha’awar komawa Canada don zama , karatu ko aiki a hukumance.

Sakon yana cewa: Takardun neman bisar CANADA na 2021/2022 sun fito

Yin rajistan neman samun bisar 2021/2022 a yanar gizo shi ne hanya mafi sauri wa duk mai sha’awar samun takardun izinin zama a kasar CANADA masu nagarta, dan aiki ko karatu.

Wannan shirin wanda aka fi sani da Visa Lottery Program a turance dama ce ta bayyana wa mutane 45,000 daga duk kasashen duniya su kasance cikin masu izinin zama a Canada, abin da ke nufin suna iya rayuwa , ko karatu, ko aiki a Canada.

Duk mai sha’awa na iya garzayawa zuwa shafin rajistan da ke yanar gizo

Za’a zabi wadanda suka yi nasara daga cikin duk wadanda suka yi rajista kuma rajista kyauta ne.

Kuna iya duba ko kun cancanta a nan:

https://tinyurl.com/CANADA-immigration2022”

Tantancewa

Binciken mahimman kalmomi ya nuna cewa tun shekarar 2018 wannan sakon ke yawo, dan haka ne ma ofishin jakadancin Canada ya fitar da sanarwar da ta nisanta shi daga sakon a shafin shi na Facebook, inda ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji fadawa hannun masu zamba cikin aminci domin a duk sadda aka nemi ofishin jakadancin a shafin bincike na google sunan wani mutun ne ake gani mai wata lambar waya ta bogi.

Da muka kara bincike mun gano cewa shafin da sakon ya ce a je a yi rajista ba shi ne halataccen shafin da ofishin jakadancin Canada ke amfani da shi ba.

Bincike kan ainihin shafin bisar Canada ya fayyace cewa kasar ba ta amfani da caca ko kuma Lottery wajen bayar da bisa. A nan ma ofishin ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji fadawa tarkon miyagu domin gwamnatin Canada ba ta bayar da bisa ta hanyar lottery inda ta ce ba ta taba fitar da wani abin da ke kama da irin takardun da sakon ke ambata ba.

“Ku kula cewa shafin canadavisa.com ba ta da wata alaka da wadannan shafukan da ke yaudarar jama’a domin gwamnatin Canada ba ta bayar da bisa ta hanyar lottery ko caca kuma takardun da aka alkawarta duk karya ne,” suka ce

A karshe

Sakamakon binciken bin diddigi na Dubawa ya nuna cewa gwamnatin Canada ba ta da alaka da wannan shafi da kuma tallar gasar cin bizar zama a kasar. Saboda haka a yi hattara.


Source link

Related Articles

32 Comments

  1. 357696 46495Hey! Do you know if they make any plugins to help with SEO? Im trying to get my weblog to rank for some targeted keywords but Im not seeing extremely good outcomes. In the event you know of any please share. Thanks! 905247

  2. 696807 347484After study several with the content material inside your web site now, we genuinely such as your technique of blogging. I bookmarked it to my bookmark web web site list and will also be checking back soon. Pls look at my web-site likewise and make me aware what you believe. 913115

  3. 659796 286710If your real friends know you as your nickname, use that nickname as your very first name online. When you very first friend someone, focus on creating a private comment that weaves connection. 626676

  4. I carry on listening to the news update lecture about getting boundless online grant applications so I have been looking around for the top site to get one. Could you tell me please, where could i acquire some?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news