Labarai

Hedikwatar tsaron ta umurci rundunonin soji su kori sojojin Nigeriya marasa da’a

Hedikwatar tsaro ta fitar da wani gargadi ga wasu jami’anta da ake zargi da nuna rashin da’a da nuna wasu munanan dabi’u.

Har ila yau, ta umurci shugabannin sojojin Najeriya, na ruwa da na sama, da su ‘kori’ jami’an da basu da kwarin guiwa a kansu, wajen sauke nauyin da ke kansu na hidimtawa kasa.

Umarnin na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Mayun da ya gabata, mai dauke da sa hannun daraktan harkokin gudanarwa na ma’aikatar tsaron Najiyar Rear Admiral Muhammed Nagenu, a madadin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor.

Shima kakakin ma’aikatar Major Akpon ya tabbatar da wannan wasika, sai dai ya ce ba wai za a kori sojojin ban aa aiki, illa dai gargadi irin na gyara kayanka, domin a cewarsa dabiu irin wadannan na iya haifar a rashin kwarin guiwa a kansu, musamman ta fuskar tura su fagen fama don tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Ta ce a yayin da take ke iya bakin kokarinta wajn yaki da matsalolin taron da ake fuskanta, rashin maida hankalin wadannan dakaru na iya maida hannun agog baya, a don haka ko su gyara, ko kuma yi musu ritayar, tunda zai rage babu wani zabi da ya uce hakan.

Birgedya Janar Sani Usman Kuka Sheka, mai sharhi ne kan lamuran tsaro a Najriya, ya kuma ce akwai abubuwan cikin gida da wasu bata gari suke fita suna yadawa ga mutanen waje, ana haka a aikin damara, amma ba a korar mutum haka kurum, sai an bi wasu hanyoyi masu yawa, kuma in da hakkokin mutum sai an biya shi hakkokinsa.

Wannan dai na faruwa ne yayin da ake unkarar zabukan 2023, kuma a cewar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, dama akan yi gargadi irin wannan a lokaci irin wannan da aka shiga harkokin siyas.

A Najeriya dai an jima ana kokakawa kan karancin jami’an tsaro, yayin da matsalolin taron ke karuwa a kasar.

Kuma wasu na kallon gargadi irin wannan a matsayin wani mafari na korar irin wadannan jami’ai da ake magana a kansu, abun da ka iya rage yawanus, maimakon karawa, matakin da ake ganin dole sai an dauka kafin iya shawo kan matsalar.


Source link

Related Articles

3 Comments

 1. Please let me know if you’re looking for a article author for your blog.
  You have some really great posts and I think I
  would be a good asset. If you ever want to take some of the load off, I’d
  really like to write some material for your blog
  in exchange for a link back to mine. Please blast me an e-mail if interested.

  Thank you!

  Stop by my webpage dent rep

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button