Nishadi

HOTUNA: ‘MATAR MUTUM KABARIN SA’: Daurin Auren Isa Suleiman da ‘Yar Amerika Janine Sanchez a Kano

A ranar Asabar ne aka daura auren Mal Isah Suleiman da masoyiyarsa Janine Sanchez, ‘yar Amerika a masallacin Juma’a dake bariki a Panshekara, jihar Kano.

Isa Suleiman, dan shekara 23 ya aure Janine Sanchez, mai shekaru 46 a Kano. An dai ruwaito cewa masoyan biyu sun hada ne a shafukan sada zumunta, shi yana Kano ita tana can Amurka. Suka rika murza soyayya har ya kai da ta yi tattaki zuwa Najeriya domin aure shi.

Cikin wadanda suka halarci wannan buki akwai fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam, kuma tsohon sanatan dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani.

Bayan an shafa fatiha, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa wannan aure da daura nuni ne na cewa soyayya bata da iyaka. Dan kano ya auri ba’Amurkiya zai dada karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu sannan da dankon soyayya.


Source link

Related Articles

69 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button