Nishadi

Hukumar NAPTIP ta cafke matar da ta shahara wajen ciniki da safarar mutane

Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) reshen jihar Edo ta cafke Mercy Owuzo mai shekara 43 da ta shahara wajen cinikayya da safarar mutane.

Kodinatan hukumar ta shiyyar jihar Edo Nduka Nwanwenne ta sanar da haka a lokacin da take zantawa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Benin a cikin wannan mako.

Nwanwenne ta ce babbar kotun tarayya dake jihar ta yanke wa Mercy hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 5 sannan za ta biya kudin tara har Naira miliyan biyu.

Ta ce hukumar ta kama Mercy da laifin tirsasa ƴan mata da shiga sana’ar karuwanci.

“Hukumar ta gano cewa Mercy na zama a Dubai da Najeriya sannan tana danfarar mutane da cewa za ta nemo musu aiki da biza a Dubai.

” Sakamakon binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa Mercy ta samu wasu mata biyu da ta yi musu karyar cewa za ta sama musu aiki a kasar Dubai.

” Kafin matan su tafi kasar Dubai sai da Mercy ta kai su wani coci inda a nan aka tsarkake su ta hanyar yi musu wanka da shafe jikinsu da mai.

“Daga nan suna isowa Dubai sai aka Kai su wani gidan haya inda Mercy ta kwace takardun tafiyan su sannan ta ce tana bin kowanen su bashin naira miliyan biyar.

“Kotu ta ce za a yi amfani da kudin da Mercy ta biya a bai wa mata biyu din da za ta tura karuwanci naira miliyan daya su raba. Sannan sauran miliyan daya za a bai wa NAPTIP domin wayar da kan mutane sanin illan tafiya zuwa kasashen waje na babu gaira babu dalili.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button