Labarai

Hukumar Tetfund ta bude wurin gwajin cutar korona a jihar Kwara

Asusun Hukumar Bunkasa Jami’o’i ta Kasa (Tetfund) ta gina wurin yin gwajin cututtuka a Jami’ar Ilorin dake jihar Kwara.

Tetfund ta gina wurin ne domin yakan cutar korona da sauran cututtuka a kasar nan.

Jami’in yada labarai na jami’ar Kunle Akogun ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai.

Akogun ya ce shugaban asusun Tetfund Sulaiman Bogoro ya kaddamar da wurin bayan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta tabbatar da ingancin wurin.

A taron kaddamarwar, Bogoro ya ce Jami’ar Ilorin na daya daga cikin jami’o’in kasar nan da ke yin bincike mai zurfin da ake amfani da su wajen bunkasa fannin kiwon lafiyar Kasar nan.

Ya kuma ce Jami’ar na da kwararrun ma’aikata da kayan aikin da suke horas da dalibai.

Bogoro ya ce asusun Tetfund na kokarin ganin ta samar da ingantattun kayan aiki a fannin kiwon lafiya domin hana kwararrun ma’aikatan lafiya ficewa zuwa kasashen waje.

Daya daga cikin matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da su shine rashin ingantattun kayan aiki.


Source link

Related Articles

112 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button