Labarai

Idan na gamsu da yadda za ka sauya fasalin Najeriya, zan dangwala maka ƙuri’a

A ranar Litinin ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya yada zangon kai ziyara a gidan fitaccen malamin nan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna.

Obi ya kai wa Gumi ziyarar ce tare da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP, Datti Baba-Ahmed, wanda dama shi ɗan asalin Jihar Kaduna ne.

Sun je Kaduna domin halartar taron tattauna batun Najeriya, wanda gamayyar wasu ƙungiyoyin Arewa su ka shirya domin tattaunawa da wasu ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Daga cikin ƙungiyoyin akwai ACF, NEF, ABF, ARDF da kuma Jam’iyyar Matan Arewa.

An fara tarukan a ranar Asabar, wanda Atiku Abubakar na PDP, Kola Abiola na PRP da Adewale Adeboye na SDP su ka halarta.

An shirya Bola Tinubu na APC da Rabi’u Kwankwaso na NNPP za su bayyana a ranar Litinin, amma Kwankwaso ya fasa halarta, bisa zargin cewa waɗanda suka shirya taron sun nuna ɓangarancin goyon bayan wani ɗan takara ɗan Arewa.

Yayin da Peter Obi ya kai ziyara gidan Gumi, ya nemi ƙuri’ar malamin a zaɓen 2023. Kuma ya shaida masa irin tsare-tsaren da ya yi wa Najeriya tanadi idan ya yi nasara.

Gumi ya yi murna da zuwan sa, kuma jinjina masa da tattakin da ya yi domin ya bayyana masa manufofin sa.

Sai dai kuma ya sha masa alwashin cewa idan ya gamsu da irin sauyin fasalin da zai yi wa Najeriya idan ya yi nasara, to zai dangwala masa ƙuri’a.

“Kamar yadda ka zo nan, to mu mutanen Kaduna za su so jin ra’ayin ka dangane da batun sauya fasalin Najeriya. Saboda Najeriya tun bayan samun ‘yanci ta ke sauya wa kan ta fasali har zuwa yau, amma abu ya kakare.

“Amma ni ina son jin na ka ra’ayin dangane da batun sauya fasalin Najeriya, ni kuma sai na shiga shafi na na Facebook, na ce wa jama’a ga ɗan takarar da zan dangwala wa ƙuri’a ta.” Inji Gumi.

Gumi har yau ya tambayi Obi ya zai yi da masu tayar da ƙayar bayan neman ɓallewa da kuma batun ƙuncin rayuwa, fatara da yunwa da talaucin da ya addabi marasa galihu a Najeriya.

“Ka na yawan magana kan tattalin arziki. To amma yawanci ka na maganar alkaluma ne. Shin ta yaya za ka yi tasiri wajen bunƙasa ɗimbin jama’ar da ba su da dabarun fasaha da kuma dandazon marasa ilmi?

“Ka na buga misali da Indiya. A Indiya jama’a na bin doka. Kuma sun fi mu wayewa ta ɓangaren yawan masu ilmi. To ta yaya za ka inganta tattalin arzikin Najeriya?

Obi ya jinjina wa Gumi da har ya bijiro masa da batun fasalin Najeriya. Ya ce batu ne da ke ƙarƙashin dokar ƙasa, wanda tilas sai an rungumi kowa wajen tattauna shi bisa tsarin da dimokraɗiyya ta shimfiɗa.

“Batun masu tayar da ƙayar baya a kowane ɓangare kuwa, za a tattauna da kowa domin a fahimci dalilin korafe-ƙorafen su.”

Obi ya ce talauci na daga cikin abin da ke sa ana hasala saboda an yi watsi da al’umma har ta kai su ga rungumar aikata manyan laifuka.
[10:06, 10/18/2022] Ashafa Daughter Numbers: Note:


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button