Labarai

Idan nine Allah ya ba kujerar majalisar Kaduna ta Arewa, zan rike mutane da adalci – Bello El-Rufai

Ɗan takarar kujerar majalisar Kaduna ta Arewa a majalisar Tarayya, Bello El-Rufai ya bayyana cewa idan Allah ya bashi kujerar wakilcin mutan Kaduna ta Arewa a majalisar Tarayya zai rike mutane da adalci.

A cikin wani bidiyo wanda El-Rufai ya magana kuma a ka yada shi a shafukan sada zumunta a yanar gizo, matashin ɗan takaran ya ce idan Allah yayi masa wannan kujera, zai rike mutane cikin adalci da kuma rikon amana.

Bello El-Rufai zai fafata da Sama’ila Suleiman na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023.

Sai dai kuma za a yi mumnunar gumurzu a lokacin wannan zaɓe, domin Samaila Suleiman na PDP ya lashi takobin ganin sai yaga abin da ture wa buzu naɗi a takarar wannan kujera.


Source link

Related Articles

10 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *