Labarai

IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

Kwanaki biyar bayan ‘yan ta’adda sun kai mummunan harin da su ka kashe sojoji 30, mobal 7 da wasu farar hula, kuma su ka yi garkuwa da ‘yan Chana a wuri haƙar ma’adinai, Gwamnatin Neja ta dakatar da masu haƙar ma’adinai a ƙananan hukumomi uku.

Ciki wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Matane ya sa wa hannu a ranar Litinin, ya ce an dakatar da haƙar ne saboda hare-haren ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda.

Ya ƙara da cewa wuraren da ake haƙar ma’adinai a fadin jihar sun zama matattara ko maɓuyar masu aikata manyan laifuka a cikin daji.

Matane ya ce “Gwamna Abubakar Bello ya sanar da dakatar da aikin haƙar ma’adinan a ƙananan hukumomi uku, sannan kuma ya bayar da umarni ga jami’an tsaro su kidaya dukkan wuraren ma’adinan da duk aka san su na fuskantar bazaranar mahara.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ɗaruruwan ‘yan ta’adda su ka ratsa garuruwa a sukwane, kafin su kai wa sojoji da mobal farmaki a dajin haƙar ma’adinan yankin Shiroro.

Yayin da aka tabbatar da kisan mutum 43, waɗanda su ka haɗa da sojoji 30 da mobal 7, an kuma tabbatar da ɓacewar wasu jami’an tsaron a gumurzun su da ‘yan ta’adda a daji haƙar ma’adinan da ke Ajata-Aboki, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Mazauna yankin Shiroro a ranar Alhamis ce su ka shaida wa wakilin mu yadda ‘yan bindiga su ka yi wannan mummunar aika-aikar a ƙazamin harin da aka kai ranar Laraba.

Waɗanda su ka ga irin yawan zugar ‘yan ta’adda a kan babura ɗauke da zabga-zabgan makamai su ka ratattaki dandazon wurin da ake haƙar ma’adinan, su ka kashe farar hula, sojoji, mobal da kuma arcewa da wasu mutanen da su ka haɗa har da ‘yan ƙasar Chana.

Kakakin Gamayyar Ƙungiyoyin Raya Garin Shiroro mai suna Salisu Sabo, ya ce ba a yi zaton za a kai harin ba, saboda yankin ya shafe watanni ba a ji motsin an kai masa hari ba.

Ya ce su na zaune lafiya bayan da aka girke sojoji a yankin.

Sabo ya ce kafin ‘yan ta’addar su kai ga wurin haƙar ma’adinan, sai da su ka keta ƙauyuka da dama.

Sabo ya ce an ce maharan sun riƙa kwantar wa mazauna ƙauyukan hankula, su na ce masu kada wanda ya gudu, ba su aka zo kai wa hari ba.

An ce sun bindige wani mutumin ƙauye bayan sun tambaye shi hanyar da wurin haƙar ma’adinan, amma ya tsaya ya na yi masu dawurwura.

“Yan bindigar dai an tabbatar cewa Boko Haram/ISWAP ne. Da ganin su za ka san cewa ba ‘yan Najeriya ba ne. Su na da dogon gashin gashi a zai, ga kuma huda hancin su.

“Sun wuce su na ambaton Allah, Allahu Akbar!”

Sun rabu gida huɗu. Su na sanye da rigunan sojoji, ‘yan sanda, har da na ‘yan sakai.

“Su na isa ma’dinar kawai sai suka kwashi mutanen da su ka yi garkuwa da su, daga nan su ka buɗe wuta.”

“Da su ka isa Unguwar Maji da ke Mazaɓar Erena, a can ne su ka yi arangama da sojoji.

“Sojoji da maharan sun yi gumurzun da tun wajen 4 na yammaci, amma har washegari ranar Alhamis da safe mu na jin rugugin bindigu.”

Ya ce baya ga tulin jami’an tsaron da aka kashe, har yanzu wasu sun ɓace babu labarin su.


Source link

Related Articles

3 Comments

 1. Right here is the right web site for anyone who would
  like to find out about this topic. You understand so much its almost tough to
  argue with you (not that I personally will need to…HaHa).

  You definitely put a fresh spin on a topic that’s been discussed for
  a long time. Excellent stuff, just wonderful!

 2. Nice post. I learn something totally new and
  challenging on sites I stumbleupon everyday. It’s always interesting to
  read content from other authors and use a little something from other websites.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button