Nishadi

Illolin yawaita aske gashin gaba ga mace

Likitoci sun gano wasu matsaloli da mata ka iya samu a dalilin yawan aske gashin gaba.

Mafi yawan mata na aske gashin gaban su ne domin tsaftace jikinsu da hana gaban su wari. Sai dai kuma likitoci sun ce yin haka ba shine ke hana gaban mace datti ba ko kuma ya rika doyi.

Sun ce mace za ta iya tsaftace gabanta idan tana yin tsarki da ruwa mai tsafta ba tare da sabulu ba.

Matsalolin da mace za ta iya afkawa ciki a dalilin yawaita aske gashin gabanta sun hada da:

1. Rashin samun gamsuwa wajen jima’i

Aske gashin gaba na iya hana mace samun gamsuwa a jima’i domin gashin gaba na fitowa ne akan jijiyoyin dake taimaka wa mace wajen samun gamsuwa a jima’i inda yawan aske gashin ke hana jijiyoyin aiki.

2. Kariya daga kamuwa daga cututtuka

Gashin gaba na hana kura da kwayoyin cututtuka shiga jikin mace ta farjin ta.

3. Yawan aske gashin gaba na sa mace ta kamu da kurarraji masu zafi da kaikayi.

4. Aske gashin gaba na sa gaban mace yin muni.

Bayan haka wasu likitoci jami’ar Ohio dake kasar Amurka sun bayyana cewa aske gashin gaba bashi da alaka da kamuwa da cututtukan sanyi da ke ta yawan yadawa.

Likitocin sun gano haka ne bayan gudanar da bincike a jikin mata 214 dake aske gashin gaban su kuma suke karatu a jami’ar.

Jagoran binciken Jamie Luster ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 10 bisa 100 daga wadannan mata na dauke da cutar sanyi sannan ga dukkan alamu wannan kason sun kamu da cutar ne a yawan saduwa da maza daban-daban.

Luster yace sun gudanar da wannan bincike ne domin gano ko akwai wani alaka tsakanin yawan aske gaban da kuma kamuwa da cututtuka irin na kamar yadda wasu likitoci suke gargadin mata su daina gaggawar aske gasin gaban su.

Ya ce wadannan likitoci sun bayyana cewa aske gashin gaba na sa a kamuda cutar sanyi a ganinsu wai barin gashin gaba na kare mace daga kamuwa da cututtuka irin na sanyi.

Likita Luster ya ce bayan gudanar da wannan bincike sun gano cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce amfani da kwarorron roba a lokacin da za a yi jima’I, tsaftace jiki, tsaftace dakin bahaya, gujewa yin amfani da bandakin da bashi da tsafta da dai sauran su ne hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cututtuka irin haka.


Source link

Related Articles

13 Comments

  1. best no deposit casino usa, united states online casino real money and united statesn poker 95
    download, or united statesn poker tournament

    My webpage: how to profit gambling (Chana)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button