Nishadi

Ina nan da rai na cikin koshin lafiya gadagau – Kabiru Nakwango

Fitaccen jarumin finafinan Hausa, Kannywood Kabiru Nakwango ya karyata raɗeraɗin da aka rika yaɗawa wai Allah yayi masa rasuwa.

An wayi gari ranar Litinin da labarai n wai Allah yayi wa jarumin rasuwa wanda wannan sako ya karaɗe shafikan sada zumunta a yanar gizo.

Sai dai kuma a wani bidiyo da ya wanda shi kansa Kaboru Nakwangon yaɗa an nuna shi a gonar sa a Kano rike da fatanyarsa yana waya.

Nakwango ya ce yana nan cikin koshin lafiya kuma raye.

Jarumi Abba Almustapha, shima ya saka a shafinsa cewa ya tattauna da Nakwango kuma ya tabbatar masa cewa yana gonara sa a wannan lokaci yana kuma cikin koshin lafiya.

Daga nan sai yayi kira da mutane masu yin irin haka da su daina ƙaga wa mutane mutuwa haka kawai batare da sun tabbatar ba.

Fitacciyar mai yin sharyi da tallata shirye-shiryen Hausa na Kannywood, Hassana Ɗalhat, ta yi tir da wannan ɗabi’ na wasu da ke yi wa mutane ƙagen mutuwa haka kawai.

” Idan ban manta ba, Jarumai kamar su Ali Nuhu, Sani Danja, Maryam Yahaya duk anntaba yi musu irin wannan. Ban san me nene masu yin haka suke anfana da dashi ba, haka kawai a rika yaɗa wai mutum ya rasu.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news