Labarai

INEC ta yi ƙarin haske kan hanyoyin tattara sakamakon zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin tsarin tattara sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da na’ura da hanyoyin sadarwar zamani a zaɓen 2023.

Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, a lokacin da ya ke yin ƙarin haske kan wani rahoto da aka danganta ruwayar sa daga kakakin. A rahoton dai an ce Okoye ya ce da hannu ba da na’ura ba za a tattara sakamakon zaɓen 2023.

“Sashe na 60(5) na Dokar Zaɓe ya tilasta wa Baturen Zaɓe tattarawa da aika sakamakon zaɓe, ciki har da adadin ƙuri’un da aka tantance, yawan ƙuri’un da aka jefa, da sakamakon da kowa ya samu a bisa tsarin da Hukumar Zaɓe ta tanadar.

“Daga nan kuma sai Baturen Zaɓe ya yi rikodin kuma ya bayyana sakamakon zaɓe da baki, sannan kuma ya bayar da sakamakon tare da dukkan takardun zaɓe bisa rakiyar jami’an tsaro da ejan na ‘yan takarar da su ka shiga zaɓe idan su na wurin, kamar yadda Hukumar Zaɓe ta gindaya.

“Tsokaci a nan shi ne a nan dai har yanzu kenan batun tattara sakamakon zaɓe ya zama da hannu kenan. Amma fa jami’in tattara zaɓe tilas ya tabbatar cewa adadin yawan ƙuri’un da aka jefa sun yi daidai da yawan sakamakon da ‘yan takara su ka samu a ƙuri’un da aka tantance a kowace rumfar zaɓe.” Inji Okoye.

Okoye ya sha su ka a kafafen sada zumunta bayan ya yi waɗannan kalamai.

Sai dai kuma a ranar Lahadi, Okoye ya ce an yi wa kalaman sa bahaguwar fahimta. Daga nan ya ƙara da cewa tattara sakamakon zaɓe da aika shi ta na’ura da hanyoyin aika saƙo na zamani kamar yadda aka yi a zaɓukan baya-bayan nan, ba za a canja ba, hakan za a yi a 2023.

Ya ce tsarin tattarawa da aika sakamakon zaɓe ta na’urori ya ƙara wa INEC nagarta da karsashi musamman a zaɓen Ekiti da na Jihar Osun.

Okoye ya ce, “gaba ɗayan tsarin tattara sakamakon zaɓe na nan ƙunshe cikin Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022, a Sashe na 60, 62 da kuma 64.”
Ya ce wannan tsarin kuma tun a cikin watan Afrilu aka fitar da sanarwar sa, aka raba wa dukkan masu ruwa da tsaki, sannan kuma aka yaɗa a shafin yanar gizon hukumar zaɓe.” Inji shi.

A ƙarshe kakakin na INEC ya ja hankalin jama’a cewa su guji gaggawar yanke hukunci kan wani batun ta hanyar karanta kanun labarai a jaridu kaɗai.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news