Labarai

INEC ta yi fatali da sunayen Sanata Lawan da na Akpabio, ta ce hauro da su aka yi ta katanga

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi APC cewa ba za ta amince da sunayen Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da na tsohon Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio a matsayin ‘yan takarar Sanata ba.

INEC ta ce sunayen su haramtattu ne, domin ba su tsaya takara an zaɓe su a lokacin da INEC ta tura jami’an ta domin sa ido wajen zaɓen fidda gwanin Sanatan Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba.

INEC ta ce sunayen Bashir Machina da na Udom Ekpoudom ta sani, domin su ne halastattun ‘yan takara.

APC dai ta ƙi damƙa wa INEC sunayen waɗanda su ka ci zaɓen, sai ta damƙa sunayen waɗanda ba su shiga zaɓe ba.

Lawan da Akpabio dai takarar shugaban ƙasa su ka shiga, amma sai su ka janye wa Bola Tinubu a ranar zaɓen fidda-gwanin APC.

Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ya faɗa a wata hira da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya ke cewa, “INEC ta yi fatali da sunan Lawan da Akpabio, saboda ba halastattun ‘yan takara ba ne.

“INEC ba za ta tilasta wa APC bin abinda doka ta shimfiɗa ba. Idan kuma ba ta janye sunayen su Lawan da Akpabio ta maye gurbin su da halastattun ba, to tamkar ba ta shiga zaɓen Sanatan Yobe ta Arewa da na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba kenan.

Idan mu ka koma labarin rikicin zaɓen-fidda-gwanin kuwa, cikin tsakiyar watan Yuni ne dai Machina ya ce canja sunan sa da na Ahmed Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.

Bashir Machina wanda ya lashe zaɓen fidda-gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda jam’iyyar APC ta maye sunan sa da na Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a jerin sunayen da ta miƙa a Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.

Machina ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka. Ya ce shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda-gwani, kuma ya samu ƙuri’u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.

Machina wanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.

Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda-gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai Lawan ya zabura neman kujerar takarar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya hi nasara.

Dokar Zaɓe Sashe na 31 ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.

Machina wanda ya taɓa yin ɗan majalisar tarayya a jamhuriya ta uku, ya yi gargaɗin idan ba a maida sunan sa ba, zai ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kotu.

“Ban janye ba, kuma ba zan janye wa kowa ba.

“Kuma ko da ba a maida suna na ba, idan ya shiga zaɓe, aka kai ƙara, to za a bai wa Machina haƙƙin sa.” Inji wasu lauyoyi.


Source link

Related Articles

4 Comments

 1. hello there and thank you for your info – I have definitely picked up anything new from right here.
  I did however expertise some technical issues using this site, since I experienced to reload
  the web site many times previous to I could get it to load properly.
  I had been wondering if your web hosting is OK?
  Not that I’m complaining, but slow loading instances times will often affect your placement in google and could damage your high-quality score if ads and marketing with Adwords.
  Well I’m adding this RSS to my e-mail and could look out for a
  lot more of your respective intriguing content.
  Ensure that you update this again soon.

 2. Hmm is anyone else encountering problems with the images on this blog loading?

  I’m trying to figure out if its a problem on my end or if
  it’s the blog. Any suggestions would be greatly appreciated.

 3. hi!,I love your writing very so much! percentage we keep in touch more approximately your article on AOL?
  I require an expert in this area to solve my problem.
  May be that is you! Looking ahead to look you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news