Labarai

INEC za ta kara kirkiro sabbin mazabu kafin zaben 2023

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta fara shirye-shiryen samar da karin mazabu a fadin kasar nan kafin zaben 2023.

Shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe (IVEC), Festus Okoye ya bayyana haka a Abuja kamar yadda a makon nan

Okoye ya kara da cewa a watan Agustan 2014 INEC ta gabatar da bukatar samar da karin mazabu 30, 027, inda arewacin kasar za ta samu muzabun 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin.

Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ba ta da isassun mazabu.

A wata sabuwa kuma, INEC da Rundunar ’Yan Sanda sun bayyana cewa sun shirya wa yin zaben cike gurbi a Jihar Neja.

Kwamishinan Zabe mai zama a Jihar Neja (REC), Farfesa Samuel Egwu, ya ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gama shiryawa tsaf domin gudanar da zaben cike gurbi da za a yi a Mazabar Tarayya ta Magama/Rijau da ke jihar a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2021.

Egwu ya fadi haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Minna.

Ya ce hukumar sa ta gama duk wani shirin yin zabe mai inganci da tsare gaskiya, domin kuwa ta horas da ma’aikatan zabe mutum 1,258 saboda zaben.

Ya kara da cewa masu zabe da aka yi wa rajista mutum 159,347 za su kada kuri’ar su a rumfunan zabe 307, kuma har masu zabe guda 158,624 sun karbi katin su na zabe na dindindin.

Egwu, wanda ya ce har hukumar tasa ta gama rarraba kayan da za a yi aiki da su a zaben, ya bayyana cewa ya na da tabbacin za a gudanar da zaben cikin nasara.

Ya ce: “Mun gama shirya ma’aikatan mu tare da ba su horo kan sanin makamar aiki ta yadda za su gudanar da zaɓen cikin inganci da tsare gaskiya idan ranar 6 ga Fabrairu ta zo.”

Shi ma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Neja ya bada tabbacin cewa sun gama duk wani shiri na bada tsaro a lokacin zaben ciken gurbin.

Kwamishinan, Alhaji Adamu Usman, ya fadi haka ne a lokacin zantawar sa da manema labarai a Minna a ranar Alhamis.

Usman ya ce ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro da ke jihar su na aiki tare don tabbatar da an yi zaben ba tare da wata hatsaniya ba.

Ya ce: “Mun tura isassun ma’aikata masu dauke da makamai domin inganta yanayin siyasa kafin da lokacin da kuma bayan zaben.

“Ina bada tabbaci dari bisa dari ga duk mazauna wannan mazabar masu son bin doka da oda cewa za su iya zuwa su kada kuri’un su a ranar 6 ga Fabrairu ba tare da fargabar barazana ga rayukan su ko dukiyoyin su ba.”


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button