Nishadi

Iyaye sun fara nuna damuwa kan yadda kallon ‘Cartoon’ ke neman gurbata tarbiyar ‘ya’yan su

Wasu iyaye mazauna babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, sun koka kan yadda kallon ‘Cartoon’ ke neman gurbatar tarbiyar ‘ya’yan su.

Iyayen da suka tattauna da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a yankin Kubuwa sun bayyana cewa kallon cartoon na taimakawa wajen inganta ilimin boko da kuma irin tarbiyyar da ‘ya’yan su ke samu ko dai ya gyara ko kuma ya lalata tarbiyar.

Amaka Ezukwuoke ta bayyana cewa cartoon na daga cikin abubuwan da suka taimaka mata wajen iya rainon ‘ya’yan ta sai dai a kwanakin nan gabata ta lura cewa cartoon din kuma yana karkatar da tarbiyyar ya’yan nata.

Ezukwuoke ta ce a dalilin kallon cartoon ‘ya’yan ta ba sa iya maida hankali wajen karatu kuma, ba su iya sauraron abin da iyaye kan fada sannan babu dama ka aiki yaro a duk lokacin da ya fara kallon cartoon.

“Wasu lokutta ‘yata har mafarkin cartoon din take yi da dare inda za ka ji tana yin wasu maganganun marasa kan gado da ihu.

Ta ce za ta rage yawan lokacin da take bari ‘ya’yan ta na kallon cartoon ganin yadda kallon ke kokarin cutar da rayuwar ya’yan ta.

Ita kuwa Justina Oluwa mazauniyar Apo ta ce ba za ta yadda ‘ya’yan ta su kalli cartoon ba saboda yadda turawa ke kokarin inganta muggan halaye irin su liwadi da madigo a wadannan yankunan.

“Wata rana ina kallon cartoon da yara na sai na ga yadda wasu ‘yan mata ke sunbatar juna sannan gashi kallon ya dauke hankalin ‘ya’yana gaba daya a wannan lokacin.

A ƙarshe wata malamar makaranta Ochiaka Uche ta yi kira ga iyaye da su maida hankali matuka ta hanyar sa ido a abubuwan da ‘ya’yan su ke kallo a talabijin.


Source link

Related Articles

One Comment

  1. 👉 $5,000 FREE EXCHANGE BONUSES BELOW 📈 👉 PlaseFuture FREE $3,000 BONUS + 0% Maker Fees 📈 + PROMOCODE FOR NEWS USERS OF THE EXCHANGE 👉 [M0345IHZFN] — 0.01 BTC 👉 site: https://buycrypto.in.net Our site is a secure platform that makes it easy to buy, sell, and store cryptocurrency like Bitcoin, Ethereum, and More. We are available in over 30 countries worldwide.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button