Labarai

Ja’afar Ja’afar ya yi hijira zuwa Birtaniya har sai Ganduje ya daina farautar sa

Fitaccen dan jarida, mawallafin Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar ya tattara nasa-inasa tare da iyalan sa gaba ɗaya sun koma kasar Birtaniya da zama har sai ya gamsu babu mai bibiyar rayuwar sa.

A hira da yayi da PREMIUM TIMES ranar Lahadi, Ja’afar ya bayyana cewa hankalin sa ba a kwance ya ke ba a kullum a kasar nan tun bayan ganowa da yayi lallai ana farautar sa.

” Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu tabbacin cewa gwamnati za ta samar mini da tsaro da iyalai na da kuma bani dama a matsayina na dan jarida in rika aiki na kamar yadda doka ta bani.

Ja’afar ya shaida wa PREMIUM TIMES a cukin Afirilu cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na neman sa ruwa a jallo saboda ya bidiyon da ya wallafa na karbar cin hanci daloli da aka nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karɓa.

A wata wasika da rundunar ‘yan sandan kasa ta rubuta wa Ja’afar, ta hannu A.A Elleman, dake ofishin Sufeto Janar din Najeriya, rundunar na bukatar Ja’afar ya bayyana a hedikwatar rundunar ƴan sanda ta kasa, a Abuja domin yin bayani game da wasu korafe-korafe da aka shigar a kan sa.

Waɗannan ƙorafe-ƙorafe kuwa sun haɗa da, ɓata suna, yin zagon ƙasa, shirga ƙarya da neman ingiza mutane su tada husuma da keta wa ofishin sufeto janar din ƴan sandan Najeriya rigar rashin mutunci wanda aka samu yana da hannu a ciki.

” A dalilin haka rundunar ta ke buƙatar mawallafin jaridar ya bayyana a ofishinta domin amsa wasu tambayoyi akan waɗannan Zargi.

Ja’afar ya karyata zargin ƴan sandan.

” Babu abinda ya haɗani da sufeto janar din ƴan sandan Najeriya, ban taɓa wani rubutu akan sa ba na ɓatanci ko tun a baya ma. Rufa-rufa kawai ake yi min, idan na bayyana hedikwatar ƴan sandan sai su damke ni.

Idan ba a manta ba jaridar Daily Nigerian ce ta fara wallafa wasu bidiyo da ke nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karkacewa ya na cusa bandir din daloli a aljufan kaftanin sa.

Ana zargi wadannan kuɗaɗe da gwamna Ganduje ke karɓar su daga hannun wani dan kwangila ne da ya ke mika masa kason sa na cin hancin wata kwangila da gwamnatin jihar ta ba su.


Source link

Related Articles

6 Comments

 1. I was wondering if you ever thought of changing the structure of your website?
  Its very well written; I love what youve got to say. But maybe you could a little more in the way
  of content so people could connect with it better.
  Youve got an awful lot of text for only having 1 or two images.
  Maybe you could space it out better?

 2. 180125 192403Wow, incredible weblog layout! How long have you been blogging for? you make blogging look simple. The overall look of your web site is wonderful, as properly as the content material! xrumer 628855

 3. Today, while I was at work, my sister stole my iPad and tested to see if it can survive a 40 foot drop, just so she can be a youtube sensation. My apple ipad is now destroyed and she has 83 views. I know this is entirely off topic but I had to share it with someone!

 4. you’re in point of fact a just right webmaster.
  The website loading velocity is incredible. It kind of feels that you’re doing any unique trick.
  Also, The contents are masterwork. you have performed a wonderful process on this subject!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news