Labarai

JAMB ta bayyana makin da Dalibi zai samu domin shiga manyan makarantun Najeriya

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) da masu ruwa da tsaki a harkar gudanarwa na manyan makarantun kasar nan sun amince da maki 140 a matsayin mafi karancin maki na shiga jami’o’i da manyan makarantun kasar nan na shekarar 2022.

Makin da aka yanke wa kwalejojin kimiyya da fasaha ya fara daga 100.

JAMB ta cimma wannan matsaya a taron tattauna tsarin shiga jami’o’i da manyan makarantu domin karatun digiri, Karatun koyon aikin malunta NCE da kuma difloma ta kasa (ND) da ke gudana a Abuja.

Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ke jagorantar wannan taro.

Adamu ya gargadi manyan makarantun Najeriya game da shiga jami’o’in ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa dole ne jami’o’i, Kwalejojin Kimiyya da Fasaha da kwalejojin ilimi su rika daukar dalibai bisa ga tsarin ‘Central Admission Processing System (CAPS)’.

Ministan ya ce duk shugaban jami’ar da aka samu yana daukar dalibai ba bisa ka’ida ba, za a gurfanar da shi a gaban kuliya ko da an gano laifin da aka aikata bayan wa’adinsa ne.

A wajen taron, an cimma matsaya cewa “Kowacce jami’a na da damar saka mafi karancin maki bisa ga samakon jarabawar UTME da ta amince da ita don shiga jami’ar ta.

Sannan shiga jami’a kai tsaye, kowace jami’a za ta tantance adadin makin da ake buƙata don shiga kai tsaye. Duk da haka, babu wata cibiya da za ta iya ba da shawarar ko shigar da kowane ɗalibi da ke da ƙasa da maki biyu don shigarwa kai tsaye.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. Can I just say what a relief to seek out someone who actually is aware of what theyre talking about on the internet. You undoubtedly know the way to bring an issue to light and make it important. More folks have to read this and understand this aspect of the story. I cant believe youre not more popular because you positively have the gift. 안전토토사이트

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button