Labarai

Jarumta da kwarewar Pantami ya sa Jami’ar MAAUN ta raɗa wa ginin jami’ar sunan sa – Farfesa Gwarzo

Shugaban jami’ar Maryam Abacha MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa jarumta da kwarewar ministan sadarwa Farfesa Isa Pantami ya sa MAAUN ta raɗa wa ginin jami’ar suna sa.

A lokacin da yake jawabi bayan kaddamar da ginin, Farfesa Gwarzo ya ce ” Tun a lokacin da Farfesa Pantami ya zama shugaban Hukumar NITDA, ya rika lura da irin ayyukan da ya rika kawo wa wannan hukuma na cigaban hukumar da kasa baki daya.

” Bayan haka kuma yanzu ya na rike da ministan Sadarwa. Ya kawo cigaba masu ma’anar gaske a kasa Najeriya don cigaban kasa. Wannan yana daga cikin muhimman dalilan da ya sa muka ga ya dace mu mu karrama ministan ta hanyar raɗa wa ginin sashen karantar da ilimin Komfuta sunan sa.

A jawabin godiya da yayi a wajen kaddamar da ginin, Pantami ya mika godiyar ga mahukuntan jami’ar bisa wannan karamci da suka yi masa.

Ya ce duk da mukamin minista da yake rike dashi bai hana shi cigaba da ayyukan karantarwa ba.


Source link

Related Articles

2 Comments

 1. Hello there, I discovered your site via Google while searching for
  a similar matter, your website got here up, it seems to be great.
  I have bookmarked it in my google bookmarks.
  Hi there, just was alert to your blog thru Google,
  and found that it is truly informative. I’m going to watch out for
  brussels. I’ll appreciate when you continue this in future.
  Many other people might be benefited from your writing.
  Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news