Labarai

JIGAWA: Hukumar Zabe tayi watsi da dan takaran APC na zaben cike gurbi a Gwaram

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Jihar Jigawa taki amincewa da zabin cikin gida da jam’iyar APC tayi na nuna dan takara wanda zai fafata a zaben cike gurbi ta kujerar dan majalissar tarraya mai wakiltar karamar hukumar Gwaram.

INEC tace APC tayi riga malam masallaci wajen bayyana dan takaran mako daya cacal da rasuwar dan majalissa Hassan Yuguda.

Hukumar ta INEC ta bayyana hakanne a ranar laraba, bayan wata sanarwa ta APC tayi a Jigawa cewar Yusufu Galambi shi ne dan takarar ta, duk da cewa ba’ayi zaben feramare ba.

A baya, Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA, ta rawaito rasuwar Malam Yuguda, dan Jam’iyar ta APC, mai wakiltar Gwaram, wanda ya rasu a babbar Asibitin kasa dake Abuja ranar 4th, March, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Sati daya cacal da rasuwar, wata kwamiti da APC ta kafa, mai jagorancin Tsohon minista Bello Maitama-Yusuf, tace Galambi shi ne dan takararta a zaben mai zuwa ta mazabar Gwaram a majalissar tarayya dake Abuja.

Maitama-Yusuf ya shaida wa kafofin yada labarai mallakar Jihar ta Jigawa cewa masu ruwa da saki na Jam’iyar APC a Jigawa sun amince da Galambi da hau tikitin ta APC.

Yace hakan ya samu amincewar matemakin Gwamnar Jihar, Umaru Namadi, da kakakin majalissar dokuki ta Jihar, Idris Garba, da kuma mai rikon kwaryar Jam’iyar ta APC a Jigawa Umaru Dikuma.

Shugaban Hukumar INEC a Jigawa, Mahmud Isa, ya shaidawa manema labarai cewa INEC bata kaiga batun zaben cike gurbin ta Gwaram ba, saboda haka duk wata sanarwa ta APC tayi babu ruwanta kuma ya saba dokar INEC.

Mr Isa yace INEC har yanzu bata samu umarni ba daga babban offishinta dake Abuja dangane da zaben cike gurbin na Gwaram, saboda haka ita awajenta babu dan takara.

Malam Isa ya kara da cewa, idan lokacin zaben yayi sai anyi firamare kuma sai INEC ta shaida kafin dan takara zai bayyana kansa a matsayin dan takara, amma yanzu a hukumar INEC babu dan takara a zaben na cike gurbi a Gwaram.


Source link

Related Articles

129 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button