Labarai

JIGILAR KASASHEN WAJE: Za a sake bude filayen jirgin saman Kano, Enugu da na Fatakwal

Shekara daya bayan hana tashi zuwa kasashen waje daga filayen jiragen saman Kano, Enugu da na Fatakawal, yanzu kuma gwamnatin Najeriya ta aza ranar da za a sake rika tashi d filayen jiragen.

An dai rufe su ne tun cikin watan Maris, 2020 domin hana bazuwar cutar korona daga kasashen duniya.

“Za mu sake bude filin jiragen sama domin tashi zuwa kasashen waje daga Enugu a ranar 3 Ga Mayu, na Kano kuma a ranar 5 Ga Mayu, sai kuma na Fatakwal a ranar 15 Ga Mayu, 2021.”

Ministan Harkokin Sufurin Jirgen Sama, Hadi Sirika ne ya yi wannan bayani, a wurin taron bayani ga manema labarai dangane da halin da ake ciki wajen yaki da cutar korona, wanda Kwamitin Yaki da Korona na Shugaban Kasa kan gudanar duk bayan mako daya.

Bayan sake bude filayen jiragen sama na duniya cikin watan Satumba, 2020, gwamnatin Najeriya ta takaita amfani da filayen jirage biyu kadai domin tashi zuwa kasashen waje daga nan Najeriya.

Filayen da ta amince da su a lokacin har zuwa yanzu, su ne Filin Jirage na Murtala Mohammed da ke Lagos da kuma Filin Jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Sirika ya nuna cewa mutane na ta ci gaba da kiraye-kiraye da nuna damuwa da kuma kagara su ga an bude filayen jiragen uku domin su ci gaba da zirga-zirga zuwa kasashen waje.

“An sha fama da aiki wurjanjan wajen ganin an dakile cutar korona a kasar nan, kafin a kai ga cimma amincewa a sake bude wadannan filayen jirage, domin s ci gaba da jigila da zirga-zirga zuwa kasashen waje.” Inji Sirika.

Sirika ya nuna cewa babu dadi ko kadan da aka rufe filayen jiragen ba a tashi zuwa kasashen waje, saboda korona.

Sai ya kara da cewa wannan annobar korona ta yi wa harkokin sufurin jrage illa, domin ita kan ta hukuma ba ta samun kudaden shiga.

Ya kara da cewa a harkar hada-hadar sufurin jirage ta kai biyan albashi ma kusan gagara ya yi.


Source link

Related Articles

48 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button