Labarai

Ka zo mu haɗa hannu a yi tafiyar nan tare – Uba Sani ga Sha’aban

Bayan nasara da Sanata Uba Sani yayi a kotun tarayya dake Kaduna ranar Juma’a in da ta tabbatar masa da takarar kujerar gwamnan na jami’yyar APC a jihar Kaduna sanatan ya roki Sani Sha’aban da yayi hakuri ya zo su yi aika tare.

Babbar Kotun Tarayya dake Kaduna ta yanke hukuncin tabbatar wa sanata Uba Sani, ɗan takarar gwamnan Kaduna na APC kujerar takarar sa.

Idan ba a manta ba, ɗaya daga cikin ɗan takarar gwamna da ya fafata da Uba Sani a zaɓen fidda gwani ya yi korafin cewa wai ba wakilan gaskiya bane suka yi zaɓen da Uba Sani yayi nasara.

Sai dai kuma a hukuncin da kotun tarayya a garin Kaduna wanda maishari’a Mohammed Garba ya yanke, ya ce tun farko bai kamata akai maganar zaɓen fidda gwani kotu ba.

” Wannan Shari’a ba nan bane huruminta, rashin jituwa ce ta jam’iyya, domin ba akai ga za a ce wai kotu ta saka baki ba. Saboda haka wannan kotu ba za ta saurari wannan kara ba, ta yi watsi da shi.

Hakan ya tabbatar da takarar Uba cewa shine sahihin ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

A dalilin wannan hukunci na kotu, masoyan ɗan takaran sun ɓarke da biki a cikin garin Kaduna.

A takarda da ya sakawa hannu da kansa wanda ya fitar bayan yanke hukuncin, Sanata Uba ya ce a matsayin su na ƴay jam’iyya ɗaya, ya hakura su zo su hannu wuri guda don kayar da sauran abokan takarar na su na wasu jam’iyyun.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button