Ciwon Lafiya

Kada a firgita da Korona nau’in ‘Omicron’ rigakafin da ake yi na samar da kariya

Shugaban hukumar dakile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC Ifedayo Adetifa ya hori ‘yan Najeriya da su yi watsi da labaran da suke ji cewa wai maganin rigakafi baya samar wa mutane kariya daga kamuwa da cutar korona samfurin Omicron mai saurin maƙure mutum.

Adetifa ya ce har yanzu yin allurar rigakafi na daga cikin matakan samun kariya daga kamuwa da mutuwa daga cutar.

“Idan maganin rigakafi na samar wa mutum kariyar Kashi 90% daga kamuwa da sumfurin Delta maganin rigakafin zai iya samar wa mutum kariyar Kashi 80% daga kamuwa da sumfurin Omicron.

NCDC ta ce har yanzu dai babu wani rahoton wannan sabuwar cuta ta yi kisa a Najeriya, amma fa an gano sagwangwaman ta har guda 126.

“Gano sagwangwaman wannan sabuwar cuta tare da gami da fantsamar cutar a Afrika ta Kudu, hakan ya tabbatar da cewa wannan cutar ta na saurin yaɗuwa a cikin mutane.

Abin da NCDC ta sani game da sumfurin Omicron

Adetifa ya ce kamar sauran masana kimiya a duniya har yanzu babu wanda ke da masaniyar iya zafin cutar domin har yanzu ana kan gudanar da bincike akan sumfurin cutar.

Ya ce akwai fargaban cewa bisa ga yadda cutar ke rikida akwai yiwar cutar za ta yi saurin yaduwa, cutar ka iya zama zazzafa, kashe ingancin kariyar da ake samu daga allurar rigakafin da ake da su yanzu. Amma har yanzu babu wanda ke da tabbacin haka game da cutar.

“Abin da muka sani shi ne har yanzu wadanda suka kamu da cutar basu nuna alamu a jikinsu sannan har yanzu babu wanda ya mutu.

Muna bukatan lokaci domin ci gaba da gudanar da bincike kan cutar domin gano yadda cutar ke yi a jikin tsofaffi ko wadanda basu da karfin garkuwan jiki.

“Muna da masaniya cewa ci gaba da kiyaye sharuɗɗan gujewa kamuwa da cutar da yin allurar rigakafin korona na daga cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Ba Omicron ba, akwai zazzafar Korona dake tafe

Adetifa ya gargaddi ‘yan Najeriya cewa akwai yiwuwar bullowar wata zazzafar sumfurin korona dake tafe idan ba an maida hankali wajen kiyaye sharuɗɗan gujewa kamuwa da cutar ba.

Ya ce za a iya shiga cikin mummunar haɗari idan aka yi watsi da kiyaye sharuɗɗan gujewa kamuwa da cutar.

Adetifa ya ce bullowar sumfurin Omicron ya zo ne a matsayin gargaɗi ga kasashen duniya cewa har yanzu ba a yi nasara ba wajen yaki da korona ba.

“Abin godiya ne yadda cutar ba yi mana kisan kiyashi ba a kasar nan amma haka ba shine zai cutar ba zai ci gaba da yaduwa ba ko mutane ba za su kamu da cutar ba.

“Abin dake faruwa shine idan ba mun mai da hankali bane wajen dakile yaɗuwar cutar ba cutar zai ci gaba da rikiɗa har a samu zazzafar nau’in cutar da ya fi wanda ake fama da shi zafi.

“Muna kira ga mutane da su koma su ci gaba da kiyaye sharuɗɗan gujewa kamuwa da cutar tare da Yin allurar rigakafin korona domin waɗannan sune matakan da za su taimaka wajen dakile yaɗuwar cutar.


Source link

Related Articles

209 Comments

 1. Pingback: free casino online
 2. Pingback: stevia keto
 3. Pingback: keto waffles
 4. Pingback: evaluation essay
 5. Pingback: whats an essay
 6. Pingback: 3characterized
 7. Pingback: 1spectacular
 8. Pingback: naked gay dating
 9. Pingback: free netbet slots
 10. Pingback: play slots online
 11. Pingback: strictly slots buy
 12. Pingback: adult slots era

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news