Labarai

Kada fa ziyarar Tinubu wurin Obasanjo ta tayar wa Jagaban da Fani-Kayode tsohon gulando

Yayin da kamfen ɗin zaɓen 2023 ke kusantowa, zafafan kalaman da wasu ‘yan siyasa su ka riƙa yi a baya na neman zama kurwar da za ta fara bibiyar su, yadda idan ba su yi da gaske ba, maita za ta cinye su.

Cikin tsakiyar makon da ya gabata ne a ranar Laraba ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Bola Ahmed Tinubu, ya kai wa tsohon abokin gabar sa, kuma tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ziyara.

Tinubu da Obasanjo sun daɗe ana gaba, wadda tun asali ta samo tushe a farkon zangon Obasanjo ya na mulki. Musabbabin matsalar dai ita ce Tinubu ya na Gwamnan Jihar Legas ya ƙirƙiro sabbin ƙananan hukumomi, waɗanda Obasanjo ya ce Gwamnatin Tarayya da dokar ƙasa ba su amince da su ba.

Daga nan Obasanjo ya hana wa Legas kuɗaɗen ta na kason wata-wata daga Asusun Gwamnatin Tarayya. Haka kuma ya hana na dukkan ƙananan hukumomin Jihar Legas, wadda ke ƙarƙashin jam”iyyar AD a lokacin.

A zaɓen 1999, Jihohin Yarabawa ba su zaɓi PDP ba, dukkan gwamnonin su na AD ne. Amma a zaɓen 2003 PDP a ƙarƙashin Obasanjo sai da ta ƙwace jihohin Yarabawa dukkan duniya su, sai Legas ce kaɗai ta gagare shi.

Daga nan an ci gaba da gaba, adawa da ‘yar-tsama tsakanin Obasanjo da TInubu.

Cikin waɗanda su ka raka Tinubu gidan Obasanjo, har da biloniya Femi Otedola da Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Tarayya.

Duk da cewa Tinubu bai fito ya ce ya na goyon bayan takarar Tinubu ba, sai kawai Gbajabiamila ya fito ya ce, “a ziyarar mu gidan Obasanjo, abin da kunne na ya ji Obasanjo ya ce nasara a gare mu ta ke.” Haka ya faɗa wa magoya baya a Surulere, Legas.

Obasanjo ya rungumi ɗan takarar mu, ya shafa bayan sa tamkar ɗan uwan sa, kuma ya yi masa addu’a.”

Sai dai kuma a ranar Asabar Obasanjo ya ce ƙarya aka yi masa, bai ce ya na goyon bayan Tinubu 2023 ba.

Baya Ta Haihu: Ban Ce Ina Goyon Bayan Takarar Tinubu Ba – Obasanjo:

A karon farko tun bayan ziyarar da ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Bola Tinubu ya kai wa Olusegun Obasanjo a gidan sa da ke gonar sa ta Otta, a Jihar Ogun, tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo ya fito ya yi maganar kore wasu maganganu da ya ce su na yawo a kafafen sadarwa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Obasanjo, Kehinde Akinyemi ya fitar a ranar Asabar, Obasanjo ya musanta cewa ya na goyon bayan takarar Tinubu a zaɓen 2023.

Ya ce maganganun da su ka keɓe su ka tattauna batun ne na ‘yan uwantaka ba na siyasa ba.

Ya ce, “masu yaɗa cewa wai na goyi bayan takarar Tinubu, makusantan ɗan takarar ne kawai, kuma hakan da su ke yi masa cutar sa su ke yi, ba taimakon sa ba.”

Cikin sanarwar dai Akinyemi ya ce Obasanjo bai amsa yardar buƙatar da Tinubu ya yi masa ba.

“Ni ban ce ba na goyon bayan takarar sa ba, kuma ban ce masa ina goyon bayan takarar sa ba.” Cewar Obasanjo.

A ziyarar da Tinubu ya kai masa, sun shafe sa’o’i uku su na ganawa, amma kuma bayan fitowar sa, Obasanjo bai gana da manema labarai ba.

Cikin tawagar ‘yan rakiyar Tinubu akwai Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, tsoffin gwamnoni irin su Segun Osoba, Gbenga Daniel, Bisi Akande da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu.

Tsohuwar Gaba: Ba A Taɓa Yin Gogarman Ɓarawon Akwati Kamar Obasanjo Ba -Tinubu a shekarun baya:

A gefe ɗaya kuma sai masu adawa da Tinubu su ka fara watsa tsoffin munanan kalaman da Tinubu ya riƙa fesa wa Obasanjo, musamman inda ya riƙa cewa “tun da aka fara dimokraɗiyya a Najeriya ba a taɓa yin tantagaryar mai maguɗin zaɓe kamar Obasanjo ba.

“Ba a taɓa yin tantagaryar mai fashin ƙuri’u da maguɗin zaɓe kamar Obasanjo ba. Ba shi da sauran amfani, tsohon gyauto ne, kamata ya yi a watsar da shi a bola ko kwandon shara.”

Cikin 2015 ne kaɗai Obasanjo da Tinubu su ka shiga inuwar siyasa ɗaya, wato APC, lokacin da ya dawo rakiyar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, har Obasanjo ɗin ya kekketa katin sa na shaidar mamba ɗin PDP.

Lokacin kamfen ɗin shugaban ƙasa, Tinubu ya ce, “Cikin 2007, marigayi Shugaban Ƙasa Umaru ‘Yar’Adua ya ce zaɓen da ya kai shi ga nasara a 2007 cike ya ke da aikata ba daidai ba. Kuma ya yi alƙawarin gyara dokar zaɓe. Obasanjo ne kuma ya shirya zaɓen. Ba a taɓa yin gogarman ɓarawon akwati kamar Obasanjo ba. Tsohon gyauto ne a yanzu, ba shi da sauran amfani, sai a watsar a kwandon shara kawai.”

Ba lallai Tinubu ya damu da irin waɗannan tone-tonen ba. Saboda ba su kenan ba, kuma za a ci gaba da zaƙulo su ana yi masa yarfen siyasa da su.

‘Shegiyar’ Ƙafa Ke Ki Ka Saba Da Gulando: Fani-Kayode Ya Rungumi Takarar Muslim-Muslim, Bayan Ya Tsine Wa Tsarin Cikin 2015:

Mutum mai saurin rikiɗewar ra’ayi ko aƙida, kuma ɗan taratsi mai fuska biyu, Femi Fani-Kayode, yanzu dai ya na a sahun gaban yi wa Tinubu kamfen. Ko a ranar Alhamis ya canja hoton bangon shafin Tiwita ɗin sa zuwa na hoton ziyarar Tinubu a gidan Obasanjo.

Sama da shekaru shida baya, a ƙasar nan ya zama gogarman yaɗa ƙarairayi da ƙirƙirar maƙarƙashiyar cewa “ana shirya makirci maida Najeriya ƙasar Musulunci da Daular Fulani da ƙarfin tsiya.” Inji shi, ba sau ɗaya ba, sau da dama.

APC Jam’iyyar Masu Bautar Shaiɗan Ce, Kuma Majalisa Shaiɗanu Ce -Fani-Kayode a shekarun baya:

“Ai APC ba jam’iyya ba ce, matattarar masu bautar Shaiɗanu ce, kuma majalisar shaiɗanu. Ba su kawo mana komai a ƙasa ba, sai kashe-kashe, ƙazanta da gagarimar ɓarna.” Haka ya taɓa fassara APC da duk wanda ke cikin ta, kafin ya koma jam’iyyar.

A shekarun baya ya yi ƙaurin suna wajen adawa da takarar Muslim-Muslim, lokacin da Tinubu ya nemi yi wa Buhari mataimaki a zaɓen 2015. Amma yanzu ganin Tinubu ɗan ƙabilar sa ne ɗan takara, ya dawo ya na goyon bayan takarar Muslim-Muslim.

“Mun yi magana kan batun zargin maida Najeriya daular Fulani. Ai batun tuni an watsar da shi ta taga. Tunda yanzu mulki zai dawo kudu, ai magana ta ƙare.

“Yanzu na fahimci abubuwa sun canja tun da na shiga APC.

“Kuma akwai gwamnoni Kiristoci har 20. A Kudu maso Yamma gwamnoni Kiristoci ne, in banda Osun.

“Hakan na nuni da cewa babu yadda za a yi a maida Najeriya ƙasar Musulunci. Kuma APC babu ruwan ta da wannan maƙarƙashiyar.”

Sai dai kuma duk da wannan matsayar ta shi a baya, a zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC, Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya goyi baya, wanda Musulmi ne, ba Kirista ba.

2023: Har Yanzu Tinubu Bai Kakkaɓe Turɓayar Zaman Kotu A Mazaunan Sa Ba:

Babbar Kotun Tarayya ta aza ranar 12 Ga Oktoba domin yanke hukuncin ƙarar Tinubu da jam’iyyar ‘Action Allience’ (AA) ta maka shi. AA ta nemi a kori Tinubu daga tsayawa takarar zaɓen 2023.

AA ta ce Tinubu ya yi fojare na satifiket. Yayin da shi kuma Mai Shari’a Obiora Egwuatu a ranar Alhamis ɗin nan ya bai wa ɓangarorin biyu na masu ƙara da wanda ake ƙara cewa lauyoyin su su kammala gabatar da bayanan su.

Wannan magana dai ta taso ne tun daga zargin da ake yi wa Tinubu cewa ya yi fojare a 1999, lokacin da ya shiga takarar gwamnan Jihar Legas.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. I blog often and I genuinely thank you for your information. This article has
    truly peaked my interest. I will take a note of your website and keep checking for new
    details about once per week. I subscribed to
    your Feed too.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news