Labarai

‘Kada ki bari wani ko wasu su mamaye gwamnatin maigidan ki’

A hira da uwargidan shugaban kasa da Aisha Buhari ta yi da BBC, ta baiwa uwargidan shugaban kasa mai zuwa shawarar kada ta kuskura ta kyale wasu daga waje su yi wa gwamnatin mijinta babakere kamar.

Ta bata shawarar ta tsaya tsayin daka ta kare mijin ta da ga irin wadannan mutane.

Idan ba a manta ba Aisha Buhari ta rika fitowa a kafafen yada labarai ta na sukar wasu jigajigai kuma aminai da yan uwan mijinta ciki har da Mamman Daura cewa wai sun hana shugaba Buhari tabuka komai wa talakawan Najeriya.

Aisha Buhari ta rika ambatar sunan dan uwan shugaban kasa wato mijinta, Mamman Daura, ta na sukar sa cewa shine ya ke juya shugaba buhari da wasu inda ita kanta ba ta samun yadda ta ke so a gwamnatin.

A lokacin da take amsa tambayar BBC, Aisha Buhari ta ce, wanda za ta zamo uwargidan shugaban kasa mai zuwa lallai ta tashi tsaye matuka kada ta bari a yi mata yi wa mijinta katsalandan a al’amurorin sa na shugabanci.

Bayan haka ta kara da cewa lallai jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa. Sannan kuma ta ce maigidan Buhari ya yi iya kokarin sa a shugabncin Najeriya da yayi.

Da aka tambayeta ko za ta fito takara a siyasa, Aisha ta ce, zama uwargidan shugaban kasa da ta yi ya ishe ta. ba za ta yi siya sa ba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button