Ciwon Lafiya

Kada ku yadda a dirka muku rigakafin Korona, akwai buge a ciki

Sanata Dino Melaye, gargadi ‘yan Najeriya da gwamnatin Najeriya cewa kada su kuskura su biye wa turawa su amshi maganin rigakafin Korona, su dirka wa mutanen Najeriya.

Dino ya ce wannan magani ba gaskiya ba ne. Ya ce zuwa yanzu da aka dirka wa wasu a kasashen waje duk sun mutu cikin kwana uku.

” Ina kira ga mahukunta a kasar nan da na kasashen Afrika, cewa kada su yarda a shigo mana da wannan magani na Korona, domin ba gaskiya bane. Maganin kashe mutane yake yi. Ana so ne a yi gwajin shi a jikin bakaken fata, mu yi ta mutuwa.

” Muna nan a duniya Kansa, Kanjamau, Ciwon Siga na ta kashe mutane sama da shekaru 40 amma ba a taba samu rigakafin sa ba sai yanzu kwatsam kawai a ce wai an samo maganin lokaci guda. Wannan ba gaskiya bane.

Sai dai kuma Dino bai fadi ko a ina ne ya ga an mutu ba ko kuma da me ya dogara ga.

Ba shi kadai ba akwai wat ‘yar kasar Amurka wanda likita ce da ta koka kan rashin ingancin wannan magani na Korona a jikin mutane. Ta gargadi mutane kada su amshi maganin.

A Najeriya dai ana samun hau-hawan alkaluman wadanda suka kamu da cutar yanzu. Abin ya kai ga har an fara rurrufe makarantu da kuma saka dokoki domin kiyaye wa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button