Ciwon Lafiya

Kamfanin Pfizer ta hada maganin da zai kare tsoffi daga kamuwa da cutar korona

Kamfanin hada magunguna na Pfizer ya bayyana cewa ya hada maganin dake da kashi 90% na ingancin hana mutuwa da kamuwa da cutar korona a jikin tsofaffi da wadanda ke cikin hadarin kamuwa da cutar.

Kamfanin ya dakatar da gwajin ingancin maganin bayan ya gano haka ranar Juma’a.

Maganin da Pfizer ya hada ya fi wanda kamfanin Merck & Co Incoporatio suka hada ‘Molnupiravir’ wanda ya nuna cewa mutum ka iya mutuwa ko ya kwanta a asibiti bayan ya yi amfani da maganin.

Magungunan da Kamfanin Pfizer da Merck & Co Incoporatio suka hada sun hada su ne domin samar wa tsofaffi da wadanda ke cikin hadarin kamuwa da cutar kariya.

Sakamakon Bincike

Kamfanin Pfizer ya gudanar da binciken ingancin maganin da ya hada a jikin mutum 1,219 da kwayoyin cutar bai yi tsanani ba a jikinsu amma tsofaffi ne su ko masu kiba a jikinsu.

An raba mutane zuwa gida biyu inda rabi aka basu maganin da Pfizer ya hada, rabi aka basu placebo.

Sakamakon hakan ya nuna cewa kashi 0.8 na wadanda aka basu maganin da Pfizer ta hada sun kwanta a asibiti bayan kwanaki uku da shan maganin sannan babu wanda ya mutu baya kwanaki 28 da amfani da maganin.

Sai dai wadanda aka basu Placebo mutum bakwai suka kwanta a asibitin sannan mutum bakwai sun mutu.

Bayan kwanaki biyar mutum daya ne ke kwance a asibiti a rukunin wadanda aka basu maganin da Pfizer ta hada sannan a rukunin placebo mutum kashi 6.7% na kwance sannan mutum 10 sun mutu.
Kwayoyin maganin da Pfizer ta hada wanda kamfanin ke sa ran sa masa suna ‘Paxlovid’ uku ake hadawa ake ba mutum sau biyu a rana.

Maganin na dauke da sinadarin ‘protease’ wanda ke hana kwayoyin cutar korona yaduwa a jikin mutum Wanda korona ke amfani da shi domin ya habbaka a jikin mutum.

Kamfanin Pfizer ta ce ta fara gwajin ingancin maganin a jikin matasa Wanda basa cikin hadarin kamuwa da cutar amma Kuma suke kamuwa da cutar.


Source link

Related Articles

10 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button