Labarai

Kamfanin Simintin BUA ya bi sahun na Ɗangote, shi ma ya ƙara fasashin siminti

Masu masana’antun sarrafa siminti na ci gaba da gasa wa masu gina gidaje aya a kai, su na ƙara masu farashin siminti a cikin halin ƙuncin rayuwar da ake fama a ƙasar nan.

Kamfanin BUA, wanda shi ne masana’anta ta huɗu mafi ƙarfin arziki a Najeriya, ya ƙara farashin naira 200 a kan kowane buhun siminti.

Ƙarfin arzikin BUA Cement dai ya kai naira tiriliyan 2.421. Duk da alwashin da ya ɗauka a baya cewa ba zai ƙara farashi ba, a yanzu dai an yi ƙarin, domin a wasu garuruwan har naira 4,000 sayar da buhun simintin ƙwaya ɗaya. Haka binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar.

Cikin shekarar 2020 dai BUA ya samu ribar naira biliyan 72.3 gyan-gyan. A cikin watan Afrilu ya yi wa ‘yan Najeriya albishir cewa ba zai ƙara farashin buhun siminti ba.

A lokacin BUA ya ce ba zai yi ƙarin ba, duk kuwa da yawan buƙatar simintin da ake yi.

Ya ƙara da cewa, “ko farashin sa ma da ake sayar da shi a yanzu ai ya yi tsada. Saboda haka ba mu yi ƙarin naira 300 a kan kowane buhun siminti ɗaya ba.” Inji kamfanin BUA a lokacin.

Sabon Farashi:

Binciken kasuwannin sayar da siminti wanda PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa masu sayar da siminti sun ƙara kuɗi. Su kuma sun ɗora dalilin ƙarin farashin da su ka yi cewa, sun yi ƙarin saboda su ma ɗin an yi masu ƙari tun daga daffon da su ke sayo simintin.

Wani mai sayar da suminti a Lugbe da ke kan titin zuwa filin jirgin sama na Abuja, mai suna Great, cewa ya yi:

“Masu simintin ba su faɗa wa jama’a gaskiya, domin su na yin ƙarin farashi a kai a kai.”

“A baya mu na sayo buhu ɗaya naira 3,000 daga daffo. Amma a yanzu naira 3,300 mu ke sayo duk buhun simintin BUA ɗaya daga Daffo inda ake sayar wa masu sari.”

A baya mu na sayarwa naira 3,200 ko naira 3,300. Amma a yanzu naira 3,400 mu ke sayarwa.

“Saboda haka duk wanda ya ce ba a ƙara wa simintin BUA farashi ba, maƙaryaci ne.”

Sauran wurare da dama su ma sun nuna an ƙara farashi. Wasu wuraren ma har naira 3,500 ake sayarwa.

Wakilin BUA mai suna Ortega Ogra, bai amsa kiran da PREMIUM TIMES ta yi masa ba, a lokacin da aka yi ƙoƙarin jin ta bakin sa.

Sai dai a ranar Alhamis da ta gabata, Shugaban Kamfanin BUA ya bayyana cewa farashin siminti zai faɗi ƙasa warwas idan aka ƙarin masana’antu masu sarrafa siminti da yawa a ƙasar nan, domin a kullum buƙatar siminti ƙaruwa ta ke yi.”


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button