Labarai

KASAFIN JAMI’O’I DA MANYAN MAKARANTU: Buhari ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya riƙe jami’o’i ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a kashe wa jami’o’in gwamnati da manyan makarantu naira biliyan 470 a 2023.

Ya bayyana cewa kuɗaɗen sun haɗa da na farfaɗo da ilmi a jami’o’i da manyan makarantu da kuma albashin malamai da ma’aikatan jami’o’in.

Da ya ke jawabi yayin gabatar da Kasafin 2023 a Majalisar Tarayya, Buhari ya nuna rashin jin daɗin sa dangane da yajin aikin malaman jami’o’i da su ka fara tun a ranar 14 Ga Fabrairu.

Daga nan ya roƙi malaman su janye yajin aiki, tare da shan alwashin cewa gwamnati za a cika dukkan alƙawurran da ta ɗauka a jarjejeniya.

Daga nan Buhari ya ce a gaskiya a yanzu gwamnatin tarayya ba za ta iya ɗaukar nauyin kula da jami’o’iita kaɗai ba.

“A ƙasashen da su ka ci gaba, ba gwamnati kaɗai ce ke ɗaukar nauyin harkokin ilmin jami’o’in ƙasa da na manyan makarantun gaba da sakandare ba. Gwamnati da jama’a ne ke ɗaukar nauyin.” Inji Buhari.

Haka kuma Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi titina da tsawon su ya kai kilomita 1,500 -Buhari a jawabin Kasafin 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa aƙalla gwamnatin sa ta gina titina a faɗin ƙasar nan da yawan su ko tsawon su ya kai kilomita 1,500.

Buhari ya ce kuma an yi titinan ne a yankunan da ke da muhimmanci wajen inganta tattalin arzikin faɗin ƙasar nan.

Da ya ke jawabi dangane da ayyukan raya ƙasa da Buhari ya ce gwamnatin sa ta samar a cikin shekaru bakwai, ya shaida wa Majalisar Tarayya irin ayyukan da ya samar wajen tsaro, lafiya, daƙile rashawa sauran fannoni daban-daban.

Ya ce gwamnatin sa ta samar da ƙarin ƙarfin wutar lantarki da yawan ta ya kai migawatts 4000.

Batun kasafin 2023 kuwa, Buhari cewa ya yi kasafin zai sauƙaƙa matsin rayuwar da kasafin 2023 bai magance ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa kasafin 2023 da ya gabatar wa Majalisar Tarayya, zai magance matsin rayuwa, rashin aikin yi ɗin da kasafin 2022 bai magance ba.

Buhari ya ce Kasafin 2022 ya samu cikas ne dalilin kasa samun kuɗaɗen shiga yadda su ka kamata saboda cikas ɗin da aka samu daga ɓangaren fetur da gas.

Ya ce kuɗaɗen shigar da aka samu tsakanin Janairu zuwa Yuli 2022 naira tiriliyan 3.66 ne kaɗai, wato kashi 63 bisa 100 daga cikin hasashen abin da za a tara a 2022.

Ya ce rashin aikin yi da yunwa na ci gaba da damun ɗimbin jama’a, amma dai gwamnatin sa na bakin ƙoƙarin ganin ta magance tsadar rayuwa, musamman ma tsadar kayan abinci.

Ya ce tsakanin Janairu zuwa Yulin 2022, gwamnatin sa ta kashe naira tiriliyan 2.87 wajen biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya albashin su, biyan ‘yan fansho da sauran kuɗaɗen tafiyar da ayyukan ofis-ofis a ma’aikatu.

Da ya koma kan kasafi kuwa, Buhari ya ce bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 42.8.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa bashin da ke kan wuyan Najeriya ya kai naira tiriliyan 42.8.

Ya yi wannan sanarwa ce lokacin da ya ke karanta jawabin Kasafin 2023 a gaban Majalisar Tarayya, a ranar Juma’a.

Buhari ya ce abin da ake bin Najeriya bashi har zuwa watan Disamba, 2022 naira tiriliyan 39.6.

Ya ce kuɗin sun ƙaru ne a cikin shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 42.8 daga watan Janairu zuwa Yuni, wato cikin watanni shida na wannan shekara ta 2022.

Buhari ya ce gwamnatin sa ta biya kuɗaɗen tallafin fetur har naira tiriliyan 1.59 cikin wannan shekarar, tsakanin Janairu zuwa Yuni.

Da ya koma kan Kasafin 2023, Shugaba Buhari ya ce an yi kasafin Naira tiriliyan 20 51, kuma za a ciwo bashin naira tiriliyan 8:8 a 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20:51, a gaban Majalisar Tarayya.

Kasafin wanda ya gabatar a ranar Juma’a, shi ne na takwas kuma na ƙarshe a mulkin sa da ya gabatar.

A cikin jawabin sa, Buhari ya bayyana cewa za a samu giɓi na naira tiriliyan 10.78, amma kuma za a cike giɓin da kuɗaɗen bashin da za a ciwo har naira tiriliyan 8.8.

Haka nan kuma ya ce a cikin kasafin, za a kashe naira tiriliyan 6.31 wajen biyan basussuka.

Ya bayyana cewa an tsara kasafin bisa kintacen cewa Gwamantin Tarayya za ta samu kuɗin shiga har naira tiriliyan 16.87 cikin 2023. Kuma ana sa ran a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.69 a kowace rana, yayin da aka yi kintacen cewa za a riƙa sayar da kowace ganga ɗaya kan Dalar Amurka 70.

Wannan kasafin wanda aka raɗa wa suna Kasafin Rage Giɓi Da Rage Ciwo Bashi, ya nuna bai ci sunan sa ba, domin za a ciwo har naira tiriliyan 8.80 a matsayin bashi cikin 2023.

Yayin jawabin sa, Buhari ya yi bitar ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar cikin shekaru bakwai da kuma bibiyar yadda aka kashe kuɗaɗen kasafin 2022.


Source link

Related Articles

14 Comments

 1. It’s possible to win a new Garmin Tactix Watch for totally free! Enter our contest now, and you could be among the lucky few to benefit from the current functions and technology. The brand-new Tactix offers enhanced battery life, a touch screen, GPS, and HR accuracy. The brand-new Tactix also features a light that shines according to your walking cadence. The green and white torch lights shine in different patterns, and the red and blue lights are helpful when treking or running in the dark. Check this link https://bit.ly/3yr38uS

 2. Looking at this article, I miss the time when I didn’t wear a mask. safetoto Hopefully this corona will end soon. My blog is a blog that mainly posts pictures of daily life before Corona and landscapes at that time. If you want to remember that time again, please visit us.

 3. Excellent items from you, man. I have bear in mind your stuff prior to and you’re simply extremely wonderful.

  I actually like what you have received here, certainly
  like what you are stating and the way by which you are saying it.
  You make it enjoyable and you continue to care for to
  keep it smart. I cant wait to read much more from you. That is actually a
  great web site.

  Feel free to surf to my blog post :: item480494461

 4. Pretty section of content. I just stumbled upon your weblog
  and in accession capital to assert that I acquire in fact enjoyed account
  your blog posts. Anyway I’ll be subscribing to
  your augment and even I achievement you access consistently quickly.

  Take a look at my page plumbing diagram

 5. Thanks for every other wonderful article.
  The place else could anybody get that kind of information in such an ideal means
  of writing? I’ve a presentation next week, and I’m on the look for such info.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button