Labarai

KASASSAƁAR ASIWAJU: APC ta yi barazanar ladabtar da Tinubu saboda gorin da ya yi wa Buhari

Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya gargaɗi dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC su guji caccakar Shugaba Muhammadu Buhari.

Adamu ya yi wannan maganar kacokan kan Bola Tinubu, wanda a ranar Alhamis ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari a Gidan Gwamnatin Jihar Ogun, a Abeokuta.

Adamu ya yi tir da irin kalaman da Tinubu ya yi, waɗanda ya ce za a ɗauki matakin ladabtar da shi.

Adamu ya yi bayanin a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, a ranar Asabar.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dukkan ‘yan takara, inda a ƙarshe dai an amince a bar wa ɗan Kudu takarar shugaban ƙasa, kamar yadda gwamnonin Arewa su ka amince.

Baki Shi Ke Yanka Wuya: Kalaman Da Su Ka Zame Wa Tinubu Alaƙaƙai:

TINUBU YA ZARE MAKAMAN 2023: ‘Ba don ba da Buhari bai zama Shugaban Ƙasa ba’ -Inji Asiwaju:

Ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa shi ne gogarman da ya cicciɓa Muhammadu Buhari ya zama Shugaban Ƙasa a 2015 da 2019.

Tinubu ya yi wannan furuci a lokacin da ya kai wa Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ziyara, inda har ya gana tare da wakilan zaɓen ‘yan takarar APC na Jihar Ogun.

Ya je ne domin neman goyon bayan wakilan zaɓen ‘yan takara, wato deliget na jihar.

Gorin Da Tinubu Ya Yi Wa Buhari:

“Ba don ni da na tsaya bayan Buhari ba, da bai zama shugaban ƙasa ba.” Haka Tinubu ya furta a wurin.

“Buhari ya jaraba sa’a da farko, bai samu nasara ba. Ya ƙara fitowa takara a karo na biyu, ya sha kaye. Ya fito karo na uku, nan ma ya sha kaye.

“Kai, Buhari fa har kuka ya riƙa rusawa aka nuno shi a talabijin ya na cewa ba zai sake yin takara ba.

“Daga nan na je har Kaduna na same shi, na ce za ka sake yin takara, kuma za ka yi nasara. Amma fa kada ka sake ka raina wa Yarabawa hankali. Ya ce ya amince.

“Tun da Buhari ya hau bai taɓa ba ni alfarmar na ba shi wani ya naɗa minista ba. Buhari bai taɓa ba ni kwangila ba. Ban taɓa roƙon komai a wurin sa ba. To yanzu lokacin da Yarabawa za su yi mulki ne, lokaci na ne.”

Tinubu ya ce shi ne ya ɗaure wa Abiodun gindi har ya zama Gwamna kuma shi ne silar zaman Osinbajo Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Shi dai Dapo Abiodun ya nuna goyon bayan sa ne ga Yemi Osinbajo, ɗan asalin Jihar Ogun, wanda shi ma Osinbajo ɗin ya fito takara.

“Shi kan sa Gwamnan ga shi nan zaune, idan ba don Allah da kuma taimako na ba, da bai zama Gwamna a nan Jihar Ogun ba.” Inji Tinubu.

Tinubu ya kuma bada labarin yadda aka ƙi ɗaukar sa ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa a 2015, saboda wai shi Musulmi ne, kamar Buhari. Amma sai ya bada sunan Yemi Osinbajo, ya ce a ɗauke shi.

Sannan kuma ya tunatar da yadda Atiku ya garzaya ya same shi, aka ba shi takarar shugaban ƙasa a AC, haka shi ma Nuhu Ribadu aka ba shi takara a ACN.

Tinubu ya nemi wakilan zaɓe su zaɓe shi domin ya fi sauran cancanta.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. It’s a shame you don’t have a donate button! I’d without a doubt donate to this fantastic blog!
    I suppose for now i’ll settle for book-marking and adding
    your RSS feed to my Google account. I look forward to brand new updates and will talk about this website with my Facebook group.

    Talk soon!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button