Labarai

Katin zabe ne damar talaka ta karshe don zabar shugabanni nagari – Kawu Sumaila

Dan takarar Sanatan Kano ta kudu a jam’iyyar NNPP Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila yace katin zabe shi ne dama ta karshe da talaka zai amfani da ita don zabar shugabanni na gari a Nigeria.

Hon. Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne yayin wani tattaki na wayar da kan al’ummar jihar kano don fita su karbi katin zabe da a yanzu haka hukumar zabe ke yi.

Yace akwai matsaloli Masu tarin yawa da suka addabi al’ummar jihar kano da kasa baki daya, wanda kuma talakawa ba za su iya maganinsu ba sai ta hanyar zabar shugabanni nagari, kuma hakan bazai yiwuba sai da katin zabe.

“Shugabanni nagari ne kadai zasu kawo wa al’umma sauki ta fuskar samar da shugabanci nagari, samar da ingantattun dokoki, ingantaccen Ilimi,kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa da inganta rayuwar al’umma”.Inji Kawu Sumaila

Dan takarar Sanatan na Kano ta kudu ya ce mata da matasa su ne abun tausayi yanzu a Nigeria saboda su ne suka fi yawa a cikin al’umma, kuma su ne suka rasa abubuwan more rayuwa wadanda ya kamata ace suna da shi, don haka ya bukace su da su mai da hankali wajen ganin sun je sun yanki katin zabe don su zabi wadanda zasu inganta rayuwar su.

“Wajibi ne mata su fito su karbi katin zabe saboda da su ne suke zuwa asibiti domin haihuwa ko su kai yaransu to sun san halin da suke ganin asibitocinmu, kuma ya’yansu ne suke zaune ba aikin yi , da dai sauran matsaloli da dole sai sun bada gudunmawar su ta hanyar yin katin zabe domin zabar shugabanni nagari”. Inji Kawu Sumaila

Hon. Kawu Sumaila da Abba Kabir Yusuf dan takarar gwamnan jihar Kano a NNPP da sauran jiga-jigan jam’iyyar na daga cikin wadanda suka fito tattakin, wanda aka fara daga gidan Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso dake Miller Road a nan Kano.

The post Katin zabe ne damar talaka ta karshe don zabar shugabanni nagari – Kawu Sumaila appeared first on VOICE OF AREWA.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button