Labarai

Khalifa Muhammadu Sanusi ya yi tir da kisan musulmi da aka yi a Jos

Khalifa Muhammadu Sanusi, Khalifan Ɗarikar Tijjaniya ya yi tir da kisan gillan da aka yi wa musulmai matafiya mabiya ɗarikar Tijjaniya a Jos.

A wata sanarwa wanda Khalifa Sanusi ya fitar ranar Lahadi ya yi kira ga musulmai musamman ƴan tijjaniya da su kwantar da hankulan su yi hakuri.

Ga cikakken sakon a nan

JAJANTAWA DA FADAKARWAA KAN KISAN GILLAR DA AKA YI WA
YAN UWAA JIHAR PLATEAU

“Inna lillahi wa inna lihi raj’un

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki tsira da amincin Allah su kara tabbata bisa fiyayyen halitta manzon Allah sallallahu alailhi wa sallam.

Bayan haka, mun sami labari ta hanhoyi dabam dabam kuma jama’a sun ji bayanai a kafofin
labarai na kisan gillar da aka yi wa yan uwa musulmi mabiya darikar Tijaniyya a jihar Filato.

Wadannan ƴan uwan dai kamar yadda dukkan ingattattun bayanai suka nuna suna kan
hanyarsu ce ta komawa gida bayan sun halarci taron zikiri a Bauchi a gidan Maulana Sheikh
Tahir Uthman Bauchi.

Da farko muna rokon Allah madaukakin Sarki Ya yi rahama ga dukkan wadanda muka rasa tare da mika ta’aziyyar mu ga iyalansu da kuma shugabanmu Maulana Sheikh Tahir Uthman Bauchi.

Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Filato da jami’an tsaro da su tsaya a kan amanar da Allah ya ba su ta kare rayuwar al’umma, a yi cikakken binciken da zai bayyana ƴan ta’addar da suka yi wannan mummunan aikin a kuma yi musu hukuncin da ya dace.

Jamar da aka kashe yan kasa ne masu hakki kuma lallai ne a bi musu hakkinsu.

Muna kira ga ‘yan uwa ‘yan Tijjaniyya da ma jama’a gaba daya da a yi hakuri kada a dauki doka a hannu a bai wa jami’an tsaro damar yin aiki yadda ya kamata.

Muna rokon Allah ya bayyana wadanda suka yi wannan ta’addancin kuma ya ba da ikon yin
adalci.

Allah ya kawo mana karshen wadannan fitintinun kuma Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya. Muna kira ga al’umma da a ci gaba da gabatar da addu’o’i ga kasa saboda neman Allah ya kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da yalwatar rayuwa.

Assalamu alaikum wa rahamtullahi wa barakatuh.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button