Labarai

Ko jama’a su kiyaye dokokin Korona ko kuma in garkame jihar kowa ya zauna gida dole

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya gargaɗi ƴan jihar da su rika kiyayewa da bin dokokin Korona a jihar in ba haka ba kuwa zai saka dokar Kulle, kowa ya zauna gida.

Gwamna Wike ya bayyana cewa da gangar mutanen jihar suke yin watsi da bin dokokin kare kai daga kamuwa da korona a jihar.

” Saboda sakacin jama’a da yi wa dokokin kare kai daga kamuwa da Korona kunnen uwar shegu, ga shi nan sai karin waɗanda ke kamuwa da cutar ake yi a jihar sannan kuma da mutuwa da mutane ke yi.

” Ko mutane su bi doka, su rika saka takunkumi da kiyaye dokokin Korona in saka dokar Kulle a jihar kaf ɗin ta, kowa ya koma gida ya zauna sai an samu sauƙi sannan in buɗe gari.

Daga nannsai ya roki waɗanda ba su yi rigakafin cutar ba su garzaya ayi musu, cewa kin yi zai saka sauran mutane cikin matsala ne.

Sam da mutum 10,000 ne suka kamu da cutar a jihar Ribas, mutum sama da 100 kuma sun mutu.

Har yanzu ana ci gaba da samun ƙarin yaɗuwar cutar da kuma mutuwar mutane a Najeriya.

Hakan ya sa gwamnatoci ke ƙara tamke jihohin da yi wa mutanen jihar gargaɗi su kiyaye dokokin korona a koda yaushe.


Source link

Related Articles

3,442 Comments

  1. Amazing blog! Do you have any helpful hints for aspiring writers?
    I’m planning to start my own site soon but I’m a little lost on everything.
    Would you recommend starting with a free platform like
    Wordpress or go for a paid option? There are so many options out there that I’m totally confused ..
    Any ideas? Kudos!