Ciwon Lafiya

KORONA AKA RAINA KO MUTUWA AKA DAINA TSORO?: ‘Yan Najeriya sun yi watsi da ƙa’idojin NCDC kan Covid-19

Tun bayan da talakawan Najeriya su ka gano yadda aka kimshe kayan abincin tallafin korona ba a raba masu ba, su ka fara dawowa daga rakiyar duk wani kamfe da Gwamnatin Tarayya ke yi kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar korona.

Hana jama’a shiga masallatai ba tare da hana shiga cinkoson kasuwanni da wuraren kallo ko gungun taron ɗaurin aure ba, shi ma ya sa an maida duk wani bayani da gwamnati ke yi kan korona cewa duk tatsuniya ce.

Shigo da allurar rigakafin korona kyauta, alhalin an bar talakawa na mutuwa dalilin zazzaɓi da amai da gudawa saboda rashin kuɗin magani, shi ma ya sa jama’a na kallon shirin gwamnati na yaƙi da korona kamar wani ihun-ka-banza ne Gwamnantin Tarayya ke yi.

Yawan ambaton biliyoyin nairori wajen duk wani lamari na yaƙi da korona, shi ma ya sa ana kallon jami’an gwamnati sun maida batun korona wata kafar jidar maƙudan kuɗaɗe kawai.

Yayin da a kullum NCDC na bayyana adadin waɗanda korona ta kashe da waɗanda su ka kamu da cutar, shi ma ya zama abin dariya jama’a na ganin cewa gwamnati na shifcin bayyana yawan masu ɗauke da cutar korona da NCDC ke yi, kawai ana yi ne domin a wawuri kuɗi.

A taƙaice dai a Najeriya yanzu an daina damuwa da jimamin yawan waɗanda korona ta kashe ko su ka kamu da cutar. Da yawa na ganin cewa ma kawai wata mura ce mai ƙarfi.

Yawan masu mutuwa dalilin korona da ake samu a yanzu, kwata-kwata ya daina bai wa jama’a tsoro.

Tuni aka yi watsi da ɗaukar matakan kariya. A garuruwa da dama sai ka yi yawo ka gaji kafin ka ga mai sanye da takunkumin kare baki da hanci (face mask).

Ƙididdigar aka buga a yau Talata, ta nuna cewa korona ta kashe mutum 2,611, kuma rahoton ya nuna cewa kashi 90 na waɗanda korona ke kashewa, ba su yi rigakafin korona ɗin ba.

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ya ce Najeriya ta yi wa mutum miliyan 4.6 rigakafin korona allura ta farko.

Ya ce mutum 1, 875, 127 aka yi wa yi wa allura ta ta biyu.

Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ya ce aƙalla akwai buƙatar a yi wa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya allurar rigakafin korona.


Source link

Related Articles

777 Comments

  1. Pingback: 3marbles
  2. Pingback: 2obstruct
  3. Pingback: aristocrat slots
  4. Pingback: spooky slots 2015