Ciwon Lafiya

KORONA: An Umarci jihohi su kulle gidajen sharholiya da holewa da taruka

Ganin yadda korona ta sake dawowa gadan-gadan a Najeriya, gwamnatin tarayya ta bijiro da sabbin dokokin kokarin dakile fantsamar ta, duk kuwa da cewa a yanzu ne ma cutar ta fi yaduwa da saurin kama mutane.

A kan haka ne gwamnatin tarayya ta hannun Kwamitin Yaki da Cutar Korona, ya umarci jihohi su bijiro da dokokin hana taruka a jidajen giya da sauran wuraren sharholiya da tarukan nishadin hululu, inda ake haduwa a cinkushe.

Haka nan kuma an hana shiga gidajen cin abinci a zauna a ci a yi tatil, sai dai a shiga a saya, a dauka a tafi gida a ci.

Tarukan bukukuwa ma an gindaya ka’idar ceewa kada a rika wuce mutum 50.

Dama kuma wurare irin su sitadiyan har yanzu ba a bari masu kallo na shiga ba.

Sai dai kuma har yanzu tun da aka fara korona cikin Janairu har yau, ba a hana jama’a da manyan ‘yan siyasa taruwa a wurin kamfen ba.

Sannan wannan doka da aka bijiro da ita, ba ta ce a rufe masallatai da coci ba, amma kuma NCDC ta ce idan abin ya kara muni, to za a iya saka dokar kulle jama’a a gidajen su.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya umarci jihohi su dauki nauyin aikin kariya da kakaba dokokin da za su rage fantsamar cutar a cikin fadin kasar nan.

Kwamitin PTF ya sanar cewa za a dauki matakan hana yaduwar cutar gadan-gadan har tsawon nan da makonni biyar masu zuwa.

“Saboda haka an kulle dukkan gidajen giya, gidajen rawa da sauran wuraren tarurrukan nishadin hululu.

“Haka gidajen abinci du kana sanar da kulle su da gaggawa, amma banda gidajen abincin da ke dafa abinci a cikin otal-otal.

Sannan kuma an umarci ma’aikata daga mataki na 01 zuwa na 12 duk su zauna a gida. Wuraren ibada ma an ce ba a son sama da mutum 50.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda cutar ke yawan watsuwa a yanzu, fiye da lokacin da ta bayyana farkon Janairu. An kuma buga labarin yadda mutum tara ya kamu a gidan Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Korona, Boss Mustapha.


Source link

Related Articles

107 Comments

  1. Pingback: 3bloggers
  2. 659061 969436As I web website possessor I believe the content material matter here is rattling wonderful , appreciate it for your efforts. You must keep it up forever! Very good Luck. 561957

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news