Ciwon Lafiya

Korona ba ta bambance shugaban ƙasa ko talaka

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi ‘yan Najeriya dangane da matsalar annobar korona da har yau ake fama da ita a Najeriya.

Ya bayyana cewa har yau Najeriya ba ta wartsakewa daga dukan da korona ta yi wa ƙasar ta jigata ba.

Da ya ke jawabi a lokacin da ya ke gabatar da kasafin 2022, Buhari ya ce baya ga jefa ƙasar nan cikin matsin tattalin arziki da korona ta yi, cutar ta haddasa wa Najeriya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen ganin an bi hanyoyi da dama an daƙile ta.

Buhari ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin sa ya ce ta yi wajen ganin an daƙile cutar korona, an hana ta yin mummunar kisa a faɗin ƙasar nan.

Ya ce sau dai kuma har yanzu ana fama da cutar a mataki na uku, kuma gwamnatin sa na bakin ƙoƙarin ganin ta ci gaba da daƙile ta.

Da ya juyi wajen matakan da su ka kamata a ci gaba da ɗauka wajen kauce wa kamuwa ko baza ta a cikin al’umma, Buhari ya yi gargaɗin ceqa, “a ci gaba da ɗaukar matakan da gwamnati ta gindaya, domin korona babu ruwan ta da kai shugaban ƙasa ne ko talaka, duk wanda ta kama ya kamu.”

A cikin jawabin, Buhari ya taɓa batun bashin da ya ce ‘yan Najeriya na nuna damuwa a kan yawan wanda ake ciwowa.

“Duk mai tantamar bashin da mu ke ciwowa ya je kawar da shakku a kan mu.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashin da gwamnatin sa ke ciwowa bai kumbura cikin da zai rikita ƙasar nan ba.

Ya ce ayyukan da ake yi da kudaden da ake ciwowa bashi a bayyane su ke, don haka duk mai tantama zai iya fita ya yi bincike ya gani da kan sa.

Buhari ya yi wannan kalami a gaban gamayyar Sanatoci da Mambobin Majalisar Dattawa, yayin da ya ke gabatar masu da kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39.

A cikin kasafin dai ya bayyana cewa Naira tiriliyan 4.11 za a kashe su wajen biyan albashi da sauran haƙƙin tafiyar da ma’aikatan gwamnati.

Sai kuma zunzurutun Naira tiriliyan 3.61 waɗanda za su tafi wajen biyan basussukan baya, wanda gwamnati ke yi a kowane ƙarshen wata.

Buhari ya ce za a kashe Naira biliyan 579 wajen biyan haƙƙin ‘yan fansho da biyan garatuti.

Yayin da Buhari ke jawabi, ya yi bitar wasu muhimman ayyukan da gwamnatin sa ta yi a shekarar da ta gabata, sannan kuma ya jinjina wa kan sa bisa ƙoƙarin da ya yi na tsayuwar sama da minti 50 ya na jawabi wajen gabatar da kasafin 2020. Kuma ya ce a wannan ranar ma zai yi bajintar sake yin irin waccan tsayuwar.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button