Ciwon Lafiya

KORONA: Dalilin da ya sa ake samun karin wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar a Najeriya

Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya zayyano wasu dalilai da ya sa Najeriya ke samun karuwa a yawan mutanen dake mutuwa sanadiyyar kamuwa da Korona.

Mamora ya ce hakan na faruwa ne a dalilin rashin gaggauta zuwa asibiti da wadanda suka kamu ba su yi.

Ya ce kamata ya yi a rika gaggawar zuwa asibiti da zaran an ga alamun cutar a jiki ba kawai a zauna a gida ana ‘yan dabaru ba.

Bayan haka Mamora ya ce gwamnati na kokarin ganin ta wadata wuraren da ake kula da wadanda suka kamu da korana na’uran samar da iska domin bunkasa aiyukkan inganta kiwon lafiyar marasa lafiya.

Daga nan wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce rashin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar da mutane ke yi musamman a jihohi Legas, Kaduna, Filato da babban birnin tarayya Abuja na cikin dalilan da ya sa cutar ke yawan kisan mutane a kasar nan.

Kwararrun sun yi gargadin cewa yaduwar cutar zai karu fiye da yadda ake tsammani idan mutane suka ci gaba da karya sharuddan.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,354 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –712, FCT-145, Filato-117, Kwara-81, Kaduna-54, Sokoto-39, Oyo-38, Rivers-37, Gombe-21, Enugu-20, Akwa Ibom-16, Bauchi-14, Delta-14, Ebonyi-13, Anambra-9, Taraba-8, Edo-8, Kano-3, Osun-2, Ekiti-2 da Ogun-1.

Yanzu mutum 92,705 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 76,396 sun warke, 1,319 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,990 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Litini 4 ga Janairu, mutum 1,204 suka kamu a Najeriya, sannan jihohin Legas, Kaduna, Filato, Kano, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. 609555 911321omg! cant picture how quickly time pass, soon after August, ber months time already and Setempber could be the initial Christmas season in my location, I actually adore it! 155595

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news