Ciwon Lafiya

KORONA: Haɗaɗɗiyar Kungiyar IDA ta tallafa wa kasashen masu tasowa da Naira biliyan 93

Babban bankin duniya ya bayyana cewa kungiyar IDA ta ware naira biliyan 93 don tallafawa kasashen masu tasowa 73 domin aikin dakile yaɗuwar Korona.

Kungiyar ta ce ta samu wadannan kudade ta hanyar tallafi daga babban bankin duniya da kasashen da suka ci gaba 43.

IDA ta ce za ta bai wa yankin Afrika kashi 70% daga cikin waɗannan kuɗaɗe.

Kungiyar ta ce kudaden zai taimakawa musu wajen inganta kiwon lafiyar mutanen su, gyara fannin ilimin boko, samar da aikin yi, kawar da yunwa, rage matsalolin canjin yanayi, kawo karshen rikice-rikice, daidaitiwa tsakanin jinsin mata da maza da sauran su a waɗannan ƙasashe.

Shugaban babban bankin duniya David Malpass ya jinjina tallafin da suka samu daga kasashen da suka ci gaba.

Malpass ya ce a dalilin wannan kudade da suka tara kasashen dake tasowa za su samu damar farfadowa daga matsalolin da suka fada a dalilin bullowar korona sannan zai taimaka wa kasashen wajen tsara matakan da za su kare mutanen kasashen su afkawa cikin matsaloli masu tada hankali.

An kafa kungiyar IDA a shekarar 1960 domin tallafawa kasashen masu tasowa da kudaden da zai taimaka musu wajen samun ci gaba a kasashen.


Source link

Related Articles

91 Comments

  1. 382108 758175Thank you for every other informative internet site. Where else could I get that type of info written in such a perfect indicates? Ive a mission that Im just now operating on, and Ive been at the look out for such information. 644010

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news