Labarai

Kotu ta bada belin wasu mata biyu da suka sace kwayayen fitillu da suka kai naira miliyan daya

Kotun majistare dake Ojo a jihar Legas ta ba da belin mata biyu Goodness Azi mai shekaru 30 da Agnes Ejah mai shekaru 29 kan naira miliyan daya bayan an kama su da kafin Satar kwayayen fitillu a kasuwar Alaba.

Lauyan da ya shigar da karar Simon Uche ya ce Goodness da Agnes sun aikata satar ne tun a watan Faburairu

Uche ya ce matan sun saci fitillun a shagon Micheal Agazie dake kasuwar Alaba wanda farashin su zai kai naira 251,000.

Ya kuma ce bayan haka wadannan mata sun sace wa Agazie Naira miliyan 3.5.

Uche ya ce wani Michael Ele ya ce Goodness ta sace masa takarda cire kudi na bankin UBA, wayar salula Nokia da katin MTN.

Laifin da matan suka aikata ya saba wa dokar hukunta masu aikata laifuka na jihar Legas na shekarar 2015 sashe na 287 da 411.

Alkalin kotun J.K Layeni ya bada belin matan akan naira miliyan daya sannan kowacce za ta gabatar da shaidu biyu a kotu a zama mi zuwa

Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 19 ga Oktoba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news