Labarai

Kotu ta hukunta wasu masu gidan haya biyu da suka kori dan haya da iyalinsa ta karfi da tsiya

Kotun majistare dake Ojo jihar Legas ta gurfanar da wasu maza biyu masu gidan haya Chuks Okoye mai shekara 62 da Abubakar Lawal mai shekara 40 kan korar wani dan haya da iyalinsa ta karfi da tsiya.

Kotun ta gurfanar da wadannan mutane bisa laifin hada baki da korar dan haya ta karfi da tsiya.

Dan sandan da ya kawo kara Asp Simeon Uche ya ce Okoye da Lawal sun aikata haka ranar 25 ga Oktoba 202 a gidan hayan dake lamba 5 layin Tedi dake Ojo.

Uche ya ce haka kawai Lawal da Okoye suka tattara kayan dan hayan mai suna Sunday Komolafe da na iyalinsa suka watsar waje ba tare da sanin sa hayan ba.

Ya ce hakan da suka yi ya karya dokar jihar Legas na shekarar 2015 sashe 340 da 412.

Alkalin kotun Ademola Adesanya ya bada belin su akan kowanen su ya biyan Naira 250,000 sannan kowanen su zai gabatar da shaidu biyu dake biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.

Za a ci gaba da shari’a ranar 10 ga Janairu 2022.

Rikici tsakanin masu gidan haya da wadanda ke zaman gidan haya rikici ne da ya daɗe yana auku.

A lokutta da dama akan samu rashin jituwa tsakanin masu gidajen haya da masu zaman gida haya idan lokacin biya yayi shi kuma ɗan haya bashi da kuɗin biya, sannan kuma mai gida ya matsa dole sai an yi.

Ko kuma shi kansa mai gidan haya ya rika kara kudin haya na babu gaira babu dalili, sannan kuma da ƙazanta.
Irei-iren waɗannan rashin jituwa daɗaɗɗen abu ba sabo sai dai kuma abin ya kan kazanta da har sai an garzaya kotu idan aka gaza samun daidaituwa.


Source link

Related Articles

15 Comments

 1. Unquestionably consider that that you said. Your favorite
  reason appeared to be on the net the easiest factor
  to consider of. I say to you, I certainly get annoyed while folks consider worries that they just do not recognize about.
  You controlled to hit the nail upon the highest as
  smartly as outlined out the entire thing with no need side-effects , other folks can take a signal.
  Will likely be back to get more. Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button