Labarai

Kotu ta raba auren Saeed da Mujidat saboda tsananin korafi da suke wa juna

Kotun gargajiya Grade A dake Mapo a Ibadan jihar Oyo ta warware kullin auren shekara 8 tsakanin Mujidat Rafiu da Saheed saboda tsananin yawan korafin da mijin ke yi.

Alkalin kotun S.M Akintayo ta ce ta raba auren ne saboda rashin zaman lafiya a tsakanin ma’auratan.

Akintayo ta bai wa Mujidat ikon kula da ƴaƴan su biyu sannan duk wata Saheed zai rika biyan Mujidat naira 10,000 na kula da su.

Ta Kuma ce Mujidat da Saheed za su hada hannu domin ganin ‘ya’yan su sun samu ilimin boko.

A kotun Mujidat ta bayyana cewa tun da suka yi aure da Saheed ta daina samun kwanciyan hankali saboda yawan korafi da masifar sa.

Ta ce Saheed na yin korafin akan abin da bai taka kara ya karya ba.

“Saheed na bi na har shago ya zazzage ni, kowa ya san masifar sa.

“Dana ga korafin nasa ba mai karewa bane, shine na garzaya kotu ayita ta kare kawai kowa ma ya kama gabansa.

Shi kuwa Saheed ya ce yana yawan yin korafi ne a ko da yaushe saboda taurin kai da rashin biyayyar matarsa.

Ya ce duk abin da ya ce Mujidat ta yi sai ta nemi hanyar da za ta bijire wa abin sannankuma ga tsantsagwaran rashin kunya da tsageranci.

” A dalilin haka ya sa na ke yi mata balbalin bala’i a koda yaushe don ta riƙa yi min biyayya.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button