Labarai

Kotu ta umarci a maida daraktocin Hukumar NFIU da aka kora saboda sun binciki sirrin kuɗaɗen Tinubu da Atiku

Kotun Sauraren Kararraki da Bin Haƙƙin Ƙorafe-ƙorafen Ma’aiakata, ta bayar da umarnin a gaggauta maida daraktocin da NFIU ta kora, saboda samun su da laifin bin-diddigin kuɗaɗen Bola Tinubu da Atiku Abubakar.

Cikin 2021 ne aka kori daraktocin biyu, waɗanda kuma su ka garzaya kotu bayan korar su.

Mai Shari’a Rakiya Haastrup, ta yanke hukunci a ranar 3 Ga Maris, 2022 cewa an bi ta haramtacciyar hanyar da aka kauce wa dokokin Najeriya wajen korar ta su.

Rakiya ta ce daga cikin hanyoyin da aka kauce ɗin, har da rashin ba su damar kare kan su, inda haka kawai aka kore su cikin Yuni, 2021.

Kotun ta umarci Shugaban Hukumar ta NFIU ya aika wa daraktocin biyu da takardar maida su kan aikin su, kuma a biya su dukkan albashin su da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin su na watanni 9 da suka shafe a gida, bayan an kore su.

Salsalar Dalilin Korar Su Daga Hukumar NFIU:

Cikin 2020 PREMIUM TIMES ta buga cikakken labarin yadda aka dakatar da Daraktan Binciken Sirri Mohammed Mustapha da kuma Daraktan Tantancewa Fehintola Salisu, kuma Mohammed Tukur ɗin ne dai ya dakatar da su a lokacin.

An dakatar da su ne saboda sun yi gaban-gabarar zurfafa binciken safara da hada-hadar kuɗaɗen Atiku Abubakar da Bola Tinubu, ba tare da sanin hukuma ba.

Sauran zarge-zargen da Tukur ya yi wa korarrun jami’an sun haɗa da:

1. Mustapha ya yi shisshigin rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da Shugaban EFCC wasiƙa a kan wasu hada-hadar Atiku Abubakar, ba tare da Hukumar NFIU ce ta sa shi ba.

An ce wannan babban laifi ne matuƙa. Tukur ya ce hukumar NFIU ba ta ɗora alhakin binciken ayyukan hada-hadar Atiku a kan Mustapha ko ofishin sa ba.

Tukur ya kuma zargi Mustapha da aika wasiƙa ta neman waɗansu bayanai da ake zargin Tinubu da aikatawa a Amurka, maganar da tsohon batu ne.

Tsohon rikici ne wanda cikin 2011 CCB ta zargi Bola Tinubu da laifin buɗe asusun ajiya bankunan ƙasashen waje a lokacin da ya ke Gwamnan Legas daga 1999 zuwa 2007.

Sai dai kuma Kotun CCT ta kori ƙarar daga baya.

Tukur ya ce dukkan abubuwan da jami’an biyu su ka aikata, ba su nemi amincewar sa ko shawarar sa ba, a matsayin shi Tukur na Shugaban su kuma Shugaban NFIU.

Majiya ta ce tun a ranar 11 Ga Agusta Tukur ya aika masu da takardar dakatarwa da kuma gargaɗi kan binciken Tinubu da Atiku ba tare da an sa su ba.

Wata majiyar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES Hausa cewa sai da aka bai wa su biyun ɗin da aka kora damar kare kan su tukunna.

Yadda Mustapha Ya Ƙara Kira Wa Kan Sa Ruwa:

Sannan kuma an samu Mustapha da laifin haɗa baki da wani jami’in NFIU, ya riƙa karɓar albashin sa a lokacin da aka dakatar da shi.

Cikin takardar korar Mustapha an gargaɗe shi tare da umarnin ya gaggauta maida wa Gwamnatin Tarayya dukkan albashin sa da ya bi ta ɓarauniyar hanya ya karɓa a lokacin da aka dakatar da shi.

Wakilin mu ya tuntubi Mustapha da Salisu ta waya amma ba su ce komai ba. Hatta saƙon tes da aka yi masu ma ba su bada amsa ba.

Idan ba a manta ba, wani ofishin lauya na C. Chris Ekemezie & Associate ya rubuta wa ICPC ƙorafi tare dai kai ƙarar Tukur, a kan dakatarwar da ya yi wa jami’an biyu.

Lauyan ya ce “an kori jami’an biyu ne saboda sun yi ƙoƙarin saɓule wa Atiku wando a ga irin safarar kuɗaɗen sirrin da ya ke yi.”

Masana da masu sharhi da dama na ganin korar akwai siyasa a cikin ta. Sannan kuma ba a kore su bisa ƙa’ida ba.


Source link

Related Articles

14 Comments

 1. Nice post. I learn something totally new and challenging on blogs I stumbleupon everyday.

  It will always be exciting to read through articles from other
  authors and practice something from their web sites.

 2. I was pretty pleased to find this page. I want to to thank you for your time due to this fantastic read!!

  I definitely appreciated every bit of it and I have you saved as a favorite to check out new things
  in your blog.

 3. Hello everybody, here every one is sharing these kinds of familiarity, so it’s nice to read this webpage,
  and I used to pay a quick visit this website daily.

 4. Excellent blog here! Also your website loads up fast! What web host are you using?
  Can I get your affiliate link to your host?
  I wish my website loaded up as quickly as yours lol

  Feel free to surf to my homepage mobile chat

 5. I’m really loving the theme/design of your site. Do you
  ever run into any web browser compatibility issues? A number of my blog audience have complained about
  my blog not working correctly in Explorer but looks great in Chrome.
  Do you have any advice to help fix this problem?

 6. Howdy! This article couldn’t be written any better!

  Going through this article reminds me of my previous roommate!
  He always kept talking about this. I most certainly will send this article to him.
  Pretty sure he’s going to have a good read. I appreciate you for sharing!

 7. I don’t know whether it’s just me or if everybody else experiencing problems with
  your website. It seems like some of the text on your content
  are running off the screen. Can someone else please provide feedback and let me
  know if this is happening to them too? This might be a issue with my web
  browser because I’ve had this happen before. Cheers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news