Labarai

Kotu ta yanke wa ‘malamin gida’ hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an akam shi da laifin ɗirka wa ‘ƴar maigida ciki

Kotun dake sauraron kararrakin fyade da cin zarafin mata a jihar Legas ta yanke wa wani malamin gida Joseph Ibanga hukuncin daurin rai da rai bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘yar maigida mai shekaru 14 fyade da dirka mata ciki.

Alkalin kotun Abiola Soladoye ta ce ta yanke wannan hukuncin ne bisa ga hujojin da fannin da suka shigar da karar suka gabatar wanda suka tabbatar cewa malamin ya aikata wannan aika-aika da ake zargin sa da su.

Soladoye ta ce Ibanga ya rika yin lalata da yarinyar a gidan iyayen ta da gidansa har ta dauki ciki Kuma ta haihu.

“Sakamakon gwajin da aka yi wa yarinyar a asibiti ya nuna cewa malamin ne ya dirka mata ciki.

“Sannan ita yarinyar ta nuna Ibanga a matsayin malaminta wanda ke tilasta wajen yin jima’i a kullum ya zo karantar da ita.

“Iyayen yarinyar sun dauki malamin aiki saboda rashin kokarin ‘yar tasu a makaranta, sai kawai gogan naka ya maida ita farkar sa.

“Ibanga butulu ne wanda ya ci amanar wannan yarinya da ya kamata ya koyar karatu sai ya rika lalata da ita

Ta ce a dalilin haka ya sa ta yanke wannan hukunci domin ya zama domin ya zama darasi ga malamai masu aikata irin wannan laifi, na cin amanar iyayen da ke mika musu amanar yayan su.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news