Labarai

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin dauri bisa zargin yi wa ‘yar makwabcinsa fyade

Kotun majistare dake Ogundu jihar Legas ta yanke wa wani matashi mai suna Ifeanyi Onyega mai shekara 22 daurin zaman gidan kaso bayan ta kamashi da laifin yi wa ‘yar makwabcinsa mai shekara 16 fyade.

Alkalin kotun M.O. Tanimola ta yi watsi da rokon sassauci da Onyega ya yi.

Tanimola ta ce Onyega zai ci gaba da zama a kurkuku har sai ta kammala yin shawara da DPP.

Ta ce za a ci gaba da shari’a bayan 21 ga watan Otoba.

A zaman da kotun ta yi ranar Alhamis lauyan da ya shigar da kara Donjour Perezi ya ce Onyega dake zama a layin Adebimpe dake unguwan Kosofe ya aikata wannan ta’asa ranar 31 ga Yuli a gidansa.

Perezi ya ce a wannan rana Onyega ya kira ‘yar makwabcinsa cikin dakinsa domin ya aike ta amma sai ya danne ta a dakin.

Lauyan ya ce Onyega ya ja wa yarinyar kunne da idan ta fadawa wa wani abin da ya faru da ita zai kashe ta.

“Sai dai yarinyar ta fada wa mahaifiyar ta abin da ya faru inda daga nan suka kawo da kara ofishin ‘yan sanda.

Ya ce laifin da Onyega ya aikata ya saba wa dokar hukunta masu aikata miyagun aiyukka ta shekara 2015 ta jihar Legas.

Bisa ga sashe 137 na dokar hukuncin duk wanda aka kama da laifin fyade shine daurin rai da rai a kurkuku.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news