Labarai

Kotun koli ta baiwa Amerkawa damar riƙe bindiga dan kare kai

  • An kama na hannun daman Bello Turji wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Sokoto a Abuja

 

Jami’an tsaro sun cika hannu da wani matashi mai suna Musa Kamarawa, na hannun daman ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Turji. Ya bayyana sunayen masu leƙen asiri da abokan huldan da ke kai wa ƴan ta’adda Kakin jami’an tsaro, abinci da magunguna a yankin Sokoto-Zamfara.

 

A cikin wani faifan bidiyo, Kamarawa, mai shekaru 33, ya bayyana cewa ɗakin ajiyar kayan yaƙi na masu garkuwa da mutanen, babu abin da ke ciki sai tarin makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar AK 47, ƙananan bindigu, bindigogin harba roka da kuma bindigogin kakkabo jiragen sama.

 

Ya ce Turji yana da yawan ƴan ta’adda da suka bazu a yankunan da suke aikata ta’addanci.

 

 

“Turji abokina ne, kullum muna tuntubar juna kuma muna neman shawarar juna kan ayyukanmu a mafi yawan lokuta,” Kamarawa ya bayyana.

 

Ya bayyana sunan wani Dakta Abubakar Hashimu Kamarawa a matsayin wanda ke kai wa ƴan ta’addan takalma da kayan sojoji.

 

Musa Kamarawa, wanda ya ke ɗan ƙanwar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa ƴan sanda na neman yayansa Basharu saboda haɗa baki da wasu jami’an shige-da-fice wurin shigo da makamai, ya bayyana sunayen sauran waɗanda suka haɗa kai da “Yahaya, Dan Tseka, Gwandi. da Summallawa”

 

Ya ce wasu daga cikinsu da suka yi karatun kiwon lafiya su ke baiwa ƴan bindigan miyagun ƙwayoyi su ke sha kafin su fita kai hari.

 

“Pabro, ya na ɗaya daga cikinsu, ɗan ƙabilar Igbo ne wanda ya ke da shagon sayar da magunguna, sai kuma Muntari Ajiya, shi Bahaushe ne,” in ji shi.

 

Dangane da ƙarfin ikon Bello Turji, Kamarawa ya ce aƙalla mutane 100 ɗauke da makamai ne suke gadin sansaninsa.

 

“Turji na kewaye da ƴan bindiga sama da 100 daga babban sansanin sa, baya ga sauran sassan.

 

“Bambancin da ke tsakanin Kaki da suke sawa da na sojoji na gaske, shi ne datti. Koyaushe suna da datti amma sojoji na gaske sun fi tsafta a fuska,” inji shi.

 

Da yake magana kan kwamandojin Bello Turji, Kamarawa ya ce sun haɗar da ƙanin ​​Turji mai suna Doso; Sani Duna, Bello Danbuzu, Atarwatse, da sauransu.

 

Ya kuma bayyana cewa Kabiru Maniya, Alhaji Shadari na daga cikin mutanen Turji da ke sanar da shi munanan abubuwan da suka aikata ta hanyar aika masa da hotuna ta WhatsApp.

 

Kamarawa, wanda ya yi nadamar abin da ya aikata, ya sha alwashin bayar da haɗin kai ga jami’an tsaron Najeriya wajen bankaɗo duk wasu ‘yan ta’adda masu aikata laifuka a yankin.

 

An kama Kamarawa ne a Abuja tare da wani Bashar Audu, ɗan Jamhoriyar Nijar da aka kama shi da wani dilan Wiwi zai kai wa mutanen Turji.

 

Bello Turji dai matashi ne da shekarun sa ba su wuce 28 a duniya, shi ke jagorantar aiyyukan ta’addanci a jihohin Sokoto da Zamfara.

 

A lokuta daban-daban ya yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar Zamfara. Sai dai lokacin da ya ce ya buɗe tattaunawa ne malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Ahmed Gumi, ya ziyarci sansaninsa da ke Zurmi a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

 

A watan Satumban 2021 ne rahotanni suka bayyana cewa ƙasurgumin ɗan ta’addan ya mayar da hedikwatarsa ​​daga Fakai a Zurmi a jihar Zamfara zuwa Isa da ke gabashin jihar Sokoto.

 

Daga: Hausa Daily Times


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button