Labarai

Kotun Tarayya ta hana Gwamnatin Tarayya damƙa Abba Kyari hannun mahukuntan Amurka

A ranar Litinin ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke hukuncin hana damƙa dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari ga mahukuntan Amurka.

Mai Shari’a Iyang Ekwo ya bayyana cewa neman da Gwamnatin Tarayya ta yi da kotu ta amince ta a damƙa Kyari ga mahukuntan Amurka domin ya fuskanci tuhumar zargin aikata zamba, raina kotu ne kawai.

Iyang ya ce ba zai yiwu kotu a nan Najeriya ta amince a aika Kyari Amurka ba, saboda a nan ma ya na fuskantar wata tuhumar zargin laifi ce, kamar yadda Amirka ke zargin sa a can ƙasar.

Cikin 2021 dai Amirka ta aiko wasiƙar neman Najeriya ta damƙa mata Kyari domin a tuhume shi a can, idan an kama shi da laifi kuma a hukunta shi.

A nan gida Najeriya kuma, an kama Abba Kyari bayan zargin sa da hukumar NDLEA ta yi da hannu wajen safarar muggan ƙwayoyi cikin Najeriya, sai Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya rubuta wasiƙar neman kotu ta damƙa Kyari a hannun sa, domin aika shi zuwa Amurka.

Mai Shari’a Iyang ya ce sai an kammala shari’ar Najeriya sannan za a koma batun aika shi Amurka tukunna.

Ofishin Mahukuntan Amurka da ke Gundumar California ta Jihar Los Angeles dai ya bayyana cewa ranar 21 Ga Satumba za a yanke wa Hushpuppi hukunci.


Source link

Related Articles

One Comment

 1. Have you ever thought about creating an e-book or guest authoring
  on other blogs? I have a blog based upon on the same ideas you
  discuss and would really like to have you share some stories/information.
  I know my readers would enjoy your work. If
  you’re even remotely interested, feel free to
  send me an e mail.

  Here is my site romantic sms messages

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news