Labarai

KUDU TA DAGULE: Yadda aka banka wa kotuna da ofishin ‘yan sanda wuta a Imo, kafin kisan Ahmed Gulak

‘Yan bindiga sun bude wa tsohon Mashawarcin Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Ahmed Gulak wuta a Owerri.

An bindige Gulak mashawarci na Jonathan kan siyasa wuta ne a kan hanyar sa ta komawa Abuja daga Owerri.

Wani jigo a PDP, Umar Arɗo, ya buga a shafin sa na Facebook, inda ya tabbatar da mutuwar Gulak ta hanyar bindige shi da aka yi, kuma ya yi masa addu’ar neman rahama.

“Mun yi rashin ɗan’uwa kuma aboki, kuma ɗan jihar mu, Ali Gulak, wanda aka kashe a Owerri. Kafin kisan sa ya taba riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Jihar Adamawa, sannan tsohon Mashawarcin Tsohon Shugaban Kasa a Harkokin Siyasa.

“Allah ya bai wa iyalai, ‘yan uwa da abokan arzikin mamacin hakurin rashin sa. Shi kuma Allah ya gafarta masa.”

Gulak tsohon ɗan PDP ne, amma kafin zaben 2019, ya koma APC, kuma shi ne ya yi zaben-fidda-gwanin zaben Gwamnan Imo na 2019, wanda aka ce Hope Uzodinma ya lashe.

Kakakin Yaɗa Laban ‘Yan Sandan Jihar Imo, Elkanna ya tabbatar da kisan wanda aka yi wa Gulak.

Haka kuma ‘yan ƙungiyar IPOB sun tsame kan su daga zargi, IPOB ta ce babu hannun ta a ciki.

Kisan Gulak ya zo bayan an banka wa wasu kotuna wuta da kuma ofishin ‘yan sanda a jihar ta Imo.

Ofishin DPO na Atta da ke Ƙaramar Hukumar Njabane aka sa wuta.

Maharan sun riƙa ratattaka wuta kusan tsawon awa ɗaya, kafin su banka wa ofishin wuta.

Sun kuma banka wa Kotun Majistare da Babbar Kotu wuta a yankin. Kuma an ɗibga sata an kuma lalata kayyaki a wata cibiyar kula da lafiya da ke yankin.

Kakakin ‘Yan Sandan Imo, Bala Elkana ya tabbatar da hare-haren a Owerri, a cikin wata sanarwa da ya fitar.

An kuma banka wa wani ofishin ‘yan sanda na Orni da ke cikin Karamar Hukumar Owerri ta Arewa wuta.

An kai hare-haren a jajibirin dokar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya yi cewa kowa ya zauna a gida, kada ya fita.


Source link

Related Articles

62 Comments

 1. fulya escort | escort fulya – bayan escort fulya kızları
  ilet iletişim kurabilirsiniz. Böylelikle görüşme için sizlere telefon numaraları ile birlikte
  fulya eskort ilanlarını sunuyoruz.

 2. Pingback: soolantra 6 mg
 3. Howdy just wanted to give you a quick heads up. The text in your article seem to
  be running off the screen in Ie. I’m not sure if this is a format issue or something to do with browser compatibility but I figured I’d post to let you know.

  The design and style look great though! Hope you get the issue fixed soon. Cheers

 4. Pingback: stromectol cough

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button