Labarai

KUDU TA DAGULE: ‘Yan bindiga sun afkwa wa kauyen Ebonyi, sun kashe mutane da dama

A cigaba da samun rashin zaman lafiya da ake yi a yankin Kudancin Najeriya,’ yan bindiga sun afkawa kauyen Ohaukwu dake jihar Ebonyi a daren Lahadi.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Ebonyi ya bayyana cewa’ yan bindigan sun afkawa wa kauyen cikin daren Labadi ne kuma sun Kasbe mutane.

Sai dai har yanzu yan sandan ba su bada bayanan yawan wadanda aka kashe ba.

Wasu mazauna sun ce rikici ne ya kaure tsakanin wasu kauyuka biyu dake makautaka da juna, wasu kuma sun ce mahara ne suka kai hari wannan kauye. A kwai kuma wadanda suka shaida cewa wai Fulani makiyaya ne suka kai wannan mummunan hari.

Ganawan gwamnonin yankin Kudu Maso Gabas

Gwamnonin Jihohin yankin Kudu maso Gabas sun haramta kiwo sakaka a jihohin su, sannan kuma sun kafa Jami’an Tsaron Samar da Tsaro na Hadin Guiwa.

A wani taron da gwamnonin su ka shirya a Owerri, babban birninjihar Imo a ranar Lahadi, sun bayyana suna sabuwar Rundunar Hukumar Tsaron Hadin Guiwa da suka samar da suna Ebube Agu, wato ‘Damisa Ki Sabo’.

Gwamna David Omahi na Jihar Ebonyi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnaonin Jihohin kabilar Igbo ne ya yi wa manema labarai bayanin abinda taron ya kunsa.

Ya bayyana cewa an haramta yawo sakaka da dabbobi ana kiwo a jhohin yankin da su ka kunshi Imo, Anambra, Abia, Ebonyi da Enugu

Ya ce sun kafa sabouwar rundunar tsaron ta hadin guiwa ce damin karfafa tsaro a yankin.

Sannan kuma an kafa kwamitin da zai kula da ayyukan da kuma tabbatar da fara aikin jami’an tsaron na ‘Damisa Ki Sabo’.

A wurin taron, gwamnonin sun yi tir da wasu hare-hare da aka kai wa wasu hukumomin tsaro a yankin da su ka hada da Hedikwatar ‘Yan Sanda a Jihar Imo da Gidan Kurkukun Owerri na jihar Imo da sauran wasu ofisoshin ‘yan sanda.

A taron sun yi kira da a samu wanzuwar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyayi da manomi.

Sun kuma nuna goyon baya kan irin kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen dakile matsalar tsaro a fadin kasar nan.


Source link

Related Articles

50 Comments

  1. 115376 149755I discovered your website internet site on google and check a couple of your early posts. Preserve inside the top notch operate. I just extra up your Feed to my MSN News Reader. Looking for toward reading far much more of your stuff afterwards! 651646

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news