Labarai

KULLE TIWITA: Ƙungiyoyi biyar da ‘yan jarida huɗu sun maka gwamnatin Buhari gaban Kotun ECOWAS

Wasu ƙungiyoyin sa-kai da kare haƙƙin jama’a, sun maka Gwamnatin Najeriya a Kotun Ƙasashen Afrika ta Yamma mai hedikwata a Abuja, inda su ka nemi kotun ta tirsasa wa Gwamnatin Shugaba Buhari ta buɗe Tiwita daga dakatarwar da ta yi mata.

Ƙungiyoyin waɗanda su ka garzaya kotun tare da wasu ‘yan jarida huɗu, sun kuma nemi gwamnati ta biya su diyyar danne masu haƙƙi, tauye masu ‘yamci da kuma haddasa masu kasa isar da saƙonni ko karɓar saƙonni ta Tiwita da gwamnatin ta yi.

Ƙungiyoyin sun haɗa da MPA, PIN, PTCIJ, IPC da kuma TICD, tare da ƴan jaridar da su ka haɗa da David Hundeyin, Samuel Ogundipe, Blessing Oladunjoye da Nwakambi Zakari, sun ce sun ɗibga asara mai yawa a tsawon kwanakin da su ka yi ba su yi amfani da Tiwita ba, tun daga ranar 4 Ga Yuni, 2021.

Bugu da ƙari sun ce hukuncin dakatar da Tiwita da Najeriya ta ɗauka, ya kauce daga yarjejeniyar ƙasashen Afirka ta Yamma, a ƙarƙashin ECOWAS, wadda Najeriya ɗin na cikin ƙasashen da su ka ƙalla yarjejeniyar.

Sun maka Gwamnatin Najeriya gaban kotun ne tare da goyon bayan wata riƙaƙƙiyar Ƙungiyar Kare Haƙƙi da Muradun Kafafen Yaɗa Labarai da ke Landan, mai suna Media Defence.

‘Media Defence’ ta shahara wajen bai wa ‘yan jarida, ‘yan ƙasa da kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su kariya a kotu da kuma neman masu haƙƙin su.

Lauya Mojirayo Nkanga ne ya shigar da ƙarar a madadin ɓangarorin masu masu ƙarar biyu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ga kwafen takardun shigar da ƙarar mai lamba ECW/CCJ/APP/29/22 masu ɗauke da shafukan dogon Turanci har shafi 73.

Kotu ba ta kai ga sa ranar fara sauraren ƙarar ba tukunna.


Source link

Related Articles

66 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button