Labarai

Kungiyar Izala ta yi Allah-wadai da masu jingina Pantami da ta’addanci

Kungiyar JIBWIS ta yi Allah-wadai da masu jingina wa Ministan Sadarwa da Bunkasa Fasahar Zamani, Isa Pantami laifin goyon bayan ta’addanci.

Cikin wata sanarwa Da Izala ta fitar wadda Ibrahim Baba Suleiman ya buha, kuma Shugaban Kungiyar Sheikh Bala Lau ya sa wa hannu, kuma aka buga a shafin Facebook na JIBWIS, Lau ya bayyana cewa:

“Kungiyar na biye da irin tattaunawar da ke gudana musamman a kafafen sadarwar zamani game da zargin da wasu masu neman tada zaune tsaye ke yi wa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Najeriya wato Isa Pantami na cewa wai yana da ra’ayi irin na ‘yan ta’adda kuma ya na goyon bayan ta’addanci.

“Babu ko shakka wannan zargi ne marar tushe wanda ke nuna jahilci ko rashin adalcin wadanda ke yin sa musamman in an duba abubuwa kamar haka:

1. Sheikh Isa Pantami Malami ne mai kira zuwa ga bin addinin musulunci bisa tafarkin sunnar Manzon Allah (S.A.W.) , shi kuwa addinin musulunci bai yarda da ta’addanci ba ko zubar da jinanen mutane wadanda ba su ji ba, kuma ba su gani ba.

2. Duk wanda ya san Sheikh Pantami ya san cewa tsawon rayuwar sa babu abinda ya yi fada da shi irin akidar tsatstsauran ra’ayin addini. Wannan ne ma ya sa a lokuta daban daban malamin ya yi mukabala da wanda ya assasa kungiyar Boko Haram wato Muhammad Yusuf a bainar jama’a kuma ya kure shi da ingantattun hujjoji.

3. Sauye-sauyen da Sheikh Pantami ya kawo a fagen sadarwa na Najeriya sun bada gudummawa matuka wurin karya lagon ’yan ta’adda wanda hakan ya sa suka yi ta aika masa da sakonni na barazanar kisa.

4. Dr. Pantami ya kawo sababbin tsare-tsare da su ka taimaka wurin farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da ba shi kariya daga zagon kasan batattu da maciya hanci da rashawa. Irin wadannan dalilan ne da makamantan su ke sa duk mai hankali zai tamabyi kan sa cewa:

“Anya wannan bita-da-kulli da ake kokarin yi wa Sheikh Pantami ba wani salo ba ne na fada da addinin musulunci da wasu dibgaggu ke ganin cewa malaman addini komai musulunci komai kwarewar su bai cancanta su rike mukamai na gwamnati masu muhimmanci ba, irin wanda Sheikh Pantamin ke rike da shi a yayin da a gefe daya kuma ba su ganin rashin cancantar hakan ga dimbin malaman wasu addinan da ke rike da mukamai iri daban daban a cikin madafun ikon kasar?

“Anya wadanda ke ganin cewa tsare-tsaren da Pantami ya kawo na dakile cin hanci da rashawa da dabaibaye ta’addanci ba su ne ke kokarin maida martani ba ta hanyar shafa wa Pantami kashin kaji don raba shi da mukamin sa?

“Anya babu siyasa da bangaranci da nuna wariyar addini cikin wadannan kiraye-kiraye na neman Sheikh Pantami ya yi murabus musamman in mun kalli tarihin wadanda ke yin kiraye-kirayen na neman tada zaune tsaye da alakokin su da wasu manyan jagororin adawa da jam’iyyun su?

“Idan har ana yin kiraye-kirayen ne saboda kishin Najeriya da damuwa da makomar ta to me ya sa ba mu ji muryoyin masu kiran ba wurin neman a dauki mataki a kan ’yan ta’addan da suka fito fili su na barazanar raba kasa tare da alkawarin kisa ga duk wanda bai ba su goyon baya ba daga cikin jagororin yankin su?

“Me ya sa ba su yi magana ba a lokacin da wasu ’yan ta’addan suka kutsa ofisoshin ‘yan sanda a yankunan su su ka yi wa ’yan sanda kisan-gilla su ka saci makamai kuma su ka kone ofisoshin?

“A karshe Kungiyar Izala na kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da wannan zargi mara tushe, su kuma zamo masu adalci da son zaman lafiya da hakurin zama da juna.

“Mu na rokon Allah Ya zaunar da Najeriya lafiya. Ya yi riko da hannun jagororin ta zuwa ga duk abinda ya ke maslaha ga kasa. Ya kuma kare ta daga sharrin makiya.”

Sa Hannu:

Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau

Shugaban JIBWIS Na Kasa


Source link

Related Articles

56 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button