Labarai

Kungiyar Kiristoci TEKAN, ta bukaci gwamnati ta biya diyyar wadanda suka rasa rayukan su rikicin Filato

Wata kungiyar Kiristoci, ‘Fellowship of Churches of Christ in Nigeria’ ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na Jiha da su biya diyyar wadanda aka kashe a rikicin jihar Filato.

Shugaban kungiyar, Rev. Moses Ebuga, yayi wannan kiran a wani taron da kungiyar ta yi da manema labarai a ranar Litinin a garin Jos.

Kungiyar wanda aka fi sani da Tarayyan Ekklesiyoyin Kristi a Nigeriya (TEKAN), na daya daga cikin kungiyoyin dake karkashin kungiyar kiristocin Najeriya CAN.

Ebuga ya ce, mutane da yawa sun rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu na biliyoyin naira sannan da dama sun rasa gidajen su da hakan ya sa suke bukatar tallafi.

Ya ce bangarorin da rikicin ya auku na daga cikin wuraren da ba a basu tallafi daga gwamnati.

“ Muna kira ga gwamnati da ta biya diyyar ga iyalan da wadanda suka rasa rayukansu a rikicin kananan hukumomin Bokkos, Riyom, Bassa da Barkin Ladi.

“ Muna kuma kira ga Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da na jihar Filato (SEMA) da su taimaka wajen tallafawa wadanda suke cikin tsananin kunci.

Haka kuma da lalata gonaki da sauran kadarori a masarautar Miango ta karamar hukumar Bassa Ebuga ya ce “tsakanin watan Yuli zuwa Agusta, mutum 85 ne aka kashe, mutum 55 sun ji rauni kuma an kwantar da su a asibiti, an kuma Kona gidaje 1,141.

“ An lalata gonaki 2,901, an kona gidaje 1,520, iyalai 5,901 da mutum 29,805 sun rasa gidajen su a kauyuka 39 na masarautar Miango.


Source link

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button